Kungiyar NASR Ta Nemi a Kakaba Haraji Mai Yawa Kan Lemun Kwalba a Najeriya
- Wata kungiya ta bayyana bukatar a kara haraji kan kayan shaye-shaye ba na maye ba a Najeriya saboda wasu dalilai
- Kungiyar ta ce a sanya haraji mai yawa tare da daukar kudin da aka samu a sanya su a ci gaban asibitocin kasar
- A bangaren kasashen waje, kamfanonin kayan zaki a Qatar na biyan 50% na haraji, duk da haka basu karye ba
FCT, Abuja - Wata kungiyar gamayya mai daukar matakin rage shan zaki (NASR) ta yi watsi da kiran da kamfanonin samar da kayan zaki suka yi ga gwamnatin tarayya na cire haraji kan kayan shaye-shaye a kasar nan.
Kungiyar a yayin wata zanga-zanga a ranar Laraba 7 ga watan Disamba a Abuja, ta bukaci gwamnatin tarayya a madadin cire harajin ta kara shi kan kayan zaki tare da zuba kudaden da aka samu ga asibitocin kasar, Daily Trust ta ruwaito.
Wannan batu na NASR na fitowa ne daga bakin kakakinta, Omei Bongos-Ikwue, wacce tace harajin N10 kan kowance lita na kayan zaki ya riga ya bayyana dokar kudi ta 2022.
Illolin da kayan zaki ke yiwa jikin dan Adam
Ta yi bayanin cewa, yawaita shan kayan zaki na da barazana ga lafiya, kuma hakan ka iya jawo ciwon suga, ciwon zuciya, makuwa da ciwon daji, BluePrint ta ruwaito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarta:
“Najeriya ce kasa ta hudu a duniya baki daya da aka fi siyar da kayan zaki, tare da siyar da kusan lita miliyan 40 a kowace shekara.
Wannan na samar da ribar biliyoyi duk shekara ga kamfanonin ta hanyar barazana ga lafiyar ‘yan kasa.”
Misalin harajin kayan zaki a wasu kasashen waje
Gamayyar ta kuma bayyana cewa, kamfanonin kayan zaki na biyan 50% a kasar Qatar a matsayin haraji kuma kamfanonin basu karye ba.
Ta kara da cewa, kara harajin zai taimawa habakar lafiya a Najeriya ba tare da kawo tsaiko ko tasgaro ga tattalin arzikin kasar ba.
Omei ta kuma bayyana cewa, harajin zai taimawa talakawan da ke fama da rashin isasshen kudin lura da lafiya da jinyar cututtuka a Najeriya.
A farkon shekarar ne ministan kudi ta sanar da sanya harajin N10 kan kowane lita na lemun kwalba, inda aka bayyana kayayyakin da haka ya shafa.
Asali: Legit.ng