Jirgin Yakin Sojoji Ya Yi Luguden Wuta Kan Mafakar Yan Ta'adda a Kaduna

Jirgin Yakin Sojoji Ya Yi Luguden Wuta Kan Mafakar Yan Ta'adda a Kaduna

  • Jiragen yakin rundunar sojin sama sun ci gaba da matsa kaimi wurin kai hare-haren bama-bamai kan yan ta'adda a Kaduna
  • Gwamnatin Kaduna da hukumomin tsaro a 'yan kwanakin nan sun yi ikirarin hallaka yan bindiga da dama
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan yace nan gaba zasu sake fitar da sanarwa

Kaduna - Luguden wutan rundunar sojin sama ta Najeriya kan mafakar 'yan bindiga a yankunan kananan hukumomin Chikun, Igabi da Birnin Gwari ya yi sanadin sheke dandazon 'yan ta'adda a Kaduna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Laraba, 7 ga watan Disamba, 2022.

Jiragen yaki.
Jirgin Yakin Sojoji Ya Yi Luguden Wuta Kan Mafakar Yan Ta'adda a Kaduna Hoto: punchng
Asali: UGC

Sai dai kwamishinan bai fayyace ainihin lokacin da rundunar sojin ta kai waɗan nan samame ba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kassara 'yan ta'adda, sun ragargajiya maboyar 'yan bindigaa dazukan wata jiha

Aruwan ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Hukumar sojin sama ta ƙara matsa ƙaimi wajen ragargazar sansanonin yan fashin daji da mafakarsu da aka gano a yankunan jihar Kaduna."
"Bayanan da gwamnatin jiha ta samu an gano tare da ragargaza wani sansani a Riyawa, Igabi LG. Haka zalika an gano maɓoyar yan biniga a yankin Tofa, karamar hukumar Birnkn Gwari, an tashe su aiki."
"Sojin sama sun kuma agazawa abokan aikinsu Sojojin ƙasa wajen kai samame yankunan Maidaro, Dogon Dawa, Damari, Saulawa da Farin Ruwa duk a ƙaramar hukumar Birnin Gwari."

Bugu da ƙari, Mista Samuel Aruwan yace Dakarun sojin sun gudanar da bincike kan ababen hari masu ɗauke da makamai a fitacciyar hanyar nan mai hatsari da ta tashi daga Kaduna zuwa Birnin Gwari.

"Binciken ya kewaye garuruwan Buruku, Kurmin Dande, Damba, Ungwan Yako, Udawa, Manini, Kuriga, Gagafada, Kushaka, Polewire da Kamfanin Doka dake kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari, ba'a gano abin zargi ba."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaba Buhari Ya Yi Kakkausan Gargadi Ga Sojoji, Ya Basu Muhimmin Aiki 1

- Aruwan.

Daga karshe kwamishinan yace nan gaba kaɗan gwamnatin Kaduna zata sake fitar da ƙarin bayani kan nasarorin da zaran ta samu sabbin bayanai.

Sojojin Najeriya Sun Kashe ’Yan Bindiga da Dama a Wasu Manyan Dazukan Jihar Kaduna

A wani labarin kuma Sojoji sun samu nasarar tura da yawan 'yan bindiga barzahu a wasu sanannun dazuka masu hatsari a jihar Kaduna

A wata sanarwa da gwamnatin Kaduna ta fitar, tace gwarazan Sojin sun kai samame dazukan Isasu, Fatika da Makera, kuma a bayanan da suka biyo baya an yi nasara mai girma.

Gwamnatin ta bakin kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ta roki al'umma su ci gaba da baiwa jami'an tsaro goyon baya da kai masu bayanan sirri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262