2023: Ku Mutunta Hakkin Dan Adam, Mutane Za Su So Ku, Buhari Ga Sojoji

2023: Ku Mutunta Hakkin Dan Adam, Mutane Za Su So Ku, Buhari Ga Sojoji

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci rundunar sojojin Najeriya da su yi ayyukansu cikin kwarewa a yayin zaben 2023
  • Ya ce idan har sojojin Najeriya na son siye zukatan mutane, toh dole su girmama yancin dan adam
  • Buhari ya ce dole sojoji su zamo a tsakiya kamar yadda suka yi a lokacin zabukan gwamnan Osun da Ekiti

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci rundunar sojojin Najeriya da su ci gaba da zama tsaka-tsaki da kuma aiki bisa tafarkin kundin tsarin mulki don gudanar da zaben 2023 cikin nasara.

A cewar wata sanarwa daga Femi Adesina, kakakin shugaban kasa, Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 5 ga watan Disamba, yayin da yake ayyana bude taron shgugaban ma'aikatan tsaro na shekara-shekara a Sokoto, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Hukumar Sojojin Kasa Tace Zata Canja Fasalin Kai Hare-Hare A Fadin Nigeria

Buhari da sojoji
2023: Ku Mutunta Hakkin Dan Adam, Mutane Za Su So Ku, Buhari Ga Sojoji Hoto: Femi Adesina
Asali: Twitter

Shugaban kasar ya ce yana da matukar muhimmanci rundunar sojin su marawa hukumar farar hula baya ta hanyar samar da yanayi na zaman lafiya don tabbatar da nasara a zabe mai zuwa.

Buhari ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A maimaita irin kwarewar da kuka nuna wajen gudanar da zabukan jihohin Anambra, Osun da Ekiti cikin nasara a babban zaben 2023."

Shugaban kasar ya kuma roki rundunar sojin da su ci gaba da inganta ayyukansu na kare hakkin dan adam yayin aiki domin shine zai sa su samu matsuguni a zukatan jama'a, rahoton Vanguard.

Rundunar soji za ta ci gaba da kawo ci gaba sa kasar - Buhari

Buhari ya kuma jaddada cewar rundunar sojojin Najeriya za ta ci gaba da zama babbar jigo na ci gaban kasar musamman ta hanyar samar da taimakon da hukumar farar hula ke bukata.

Kara karanta wannan

Jami'iyar APC Nakasu Kawai Ta Kawo A Nigeria Tsawon Lokacin da ta Shafe Tana Mulki, Atiku

"Saboda haka wannan gwamnati ta riki wata manufa na zamanantar da rundunar sojin Najeriya da rundunonin tsaro baki daya."

Shugaban kasar ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen samar da tsaro ga yan Najeriya, yana mai cewa ana nan ana ci gaba da shirya dabaru domin bayar da tallafin da suka dace don karfafa tsaron kasar.

Babachir: Za mu tattara mu koma kasar Kamaru Idan Obi ya fadi zaben shugaban kasa

A wani labarin, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya nuna karfin gwiwa cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter obi zai doke Atiku da Tinubu a zaben 20w0.

Sai dai kuma, Babachir wanda yace babu abun da zai hana su cin zabe ya ce za su yi kaura zuwa Kamaru idan har Obi ya fadi a zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng