Kungiyar ASUU Ta Yanke Shawarar Ci Gaba Da Zanga-Zangar Lumana Sabida Gwamnati Taki Biya Musu Bukatu
- Kungiyar malaman jami'oi ta ASUU ta koka kan yadda gwamnatin tarayya taki biyanta albashin wata takwas
- Kungiyar malaman jami'io sun sami albashin watan Nuwanban da ya gabata, ba tare da rage musu ko sisi ba, duk da sauran wata takwas da suke bi
- Kungiyar dai na Shirin sake Tsunduma wani yajin aikin sakamakon abinda gwamnatin tarayya tayi, na kin cika musu alkawarin da sukai
Abuja: Membobin kungiyar ASUU, sun yanke shawarar ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana maimakon yajin aiki sakamakon kin biyansu albashin wata takwas da gwamnatin tarayya tayi.
Wannan dai na zuwa ne bayan taron da kwamitin zartawar kungiyar (NEC) tayi a garin Calabar na jihar Cross River.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wata majiya ta shaida wa Vanguard cewa taron ya kuma amince da a ci gaba da jan hankalin masu ruwa da tsaki a kan suyi kira ga gwamnati ta biya musu bukatunsu.
“A majiyar da jaridar Vanguard din ta samu, tace
Shugaban kungiyar na kasa zai fito da takardar bayan taro, duk da dai sai munji daga bakin 'ya 'yan kungiyoyin na rassanmu kafin mu yanke hukunci ci gaba da zanga-zangar. Amma dai muna tabbatar muku da cewa zamu gudanar da ita sabida yadda gwamnatin tarayya tai biris da mu duk da lokacin da muka bata".
“Wasu fitattun ‘yan Najeriya da kungiyoyi daban-daban sun yi ta kai ruwa rana da Neman mafita, muma kuma duk munyi duk abinda ya kamata, amma gwamnati taki ta kula mu, kuma jama'a suna ganin kaman mune masu laifi, amma duk da haka zamu dau matakin da muka ga ya fi dacewa,” inji majiyar.
Kotu da Kakakin Majalissar Wakilai Ne Suka Sa ASUU Janye Yajin Aikin
Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ne ya shiga tsakani, sannan kuma kotun masana’antu ta kasa da ke Abuja ta bayar da umarnin janye yajin aikin da kungiyar ta yi kafin yanzu da ke shirin komawa.
Za ku iya tuna cewa a lokacin da kungiyar ta janye yajin aikin a ranar 14 ga watan Oktoba, bayan watanni takwas da ta shafe tana yinsa.
A watan Nuwanban da ya gabata, gwamnati ta biya malaman cikakken albashinsu , yayin da kuma ta biya su rabin albashin watan Oktoba, watan da suka janye yajin aikin.
A lokuta da dama dai gwamnati ta ce ba za ta biya su albashin watanni takwas ba, sabida basu yi aiki ba.
Asali: Legit.ng