Wata Tara Bayan Dawo Da Zirga-Zirgan Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja, An Ga Ba Fasinjoji A Tashar

Wata Tara Bayan Dawo Da Zirga-Zirgan Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja, An Ga Ba Fasinjoji A Tashar

  • Gwamnati ta dawo da zirga-zirgar jiragen kasa tare da tabbatar da tsaron fasinjojin a fadin tarayya
  • An kaiwa Jirgin Harin ne a watan Uku Na Wannan Shekarar Da Muke Ciki Inda Mutane da Dama Suka rasa Ransu Wasu Kuma Suka Jikkata
  • Sakamakon Yawan Harin da 'Yan Ta'adda Ke Kaiwa Ta Hanyar Mota Yasa Jama'a Da Dama Sauya Hanaya Da Bin JIrgin Kasan

Abuja: Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta koma aiki a hanyar jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja, bayan watanni tara da harin da ‘yan ta’adda da suka kai wa jirgin hari a gari a kusa da Kaduna.

A ranar Litinin, da karfe 9:45 na safe jirgin kasa na farko, tun bayan harin, ya bar tashar Kaduna zuwa Abuja, babban birnin kasar. Kamar yadda wakilin Premium Times ya sheda tashin jirgin

Kara karanta wannan

Abj-Kad: Jirgi zai dawo aiki, IGP ya tura wasu jami'ai da manyan makamai saboda wasu dalilai

Jirgin Kasa
Wata Tara Bayan Dawo Da Zirga-Zirgan Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja, An Ga Ba Fasinjoji A Tashar Hoto: Channels TV
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An tura jami'an tsaro dauke da makamai

Kafin a koma zirga-zirgar, 'yan sanda sun sanar da sabbin matakan tsaro don tabbatar da tsaron lafiyar fasinjojin da ke kan hanyoyin.

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya bayar da umarnin tura jami’an ‘yan sanda dauke da makamai da aka zabo daga rundunar ‘yan sanda wanda suke akarkashin ofishin leken asiri na rundunar ‘yan sanda da na sashin warware bama-bamai.

Sannan an ware ‘yan sandan jirgin kasa wanda zasu ringa aiki a cikin jirgin daga Abuja zuwa Kaduna da kuma Kaduna zuwa Abuja

“Saboda haka, IGP, ya baiwa jama’a, musamman masu amfani da jirgin tabbacin samun isasshiyar kariya ta rayukan su.

Akalla mutane 9 ne suka mutu a harin yayin da aka bayyana bacewar mutane 168, wadanda aka yi imanin cewa an yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari: Litinin Din Nan Mai Zuwa Dalbai Zasu Far Zanga-Zanga Dan A Saki Aminu

Mai Ya Faru

Jirgin ya taso ne ne daga Abuja zuwa Kaduna kafin daga bisani ‘yan ta’adda su kai masa hari a a kusa da Kaduna.

Yayin da aka yi garkuwa da fasinjoji da dama da ke cikin jirgin, wasu da dama sun tsere da raunuka wanda ya yi sanadiyar mutuwarsu.

'Yan ta'addar sun sako wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a rukuninsu bayan da 'yan uwansu suka biya kudin fansa.

Sai dai jami’an ‘yan sandan farin kaya, SSS, sun kama Tukur Mamu wanda suke tunanin shine wanda ya taimaka musu da kai harin

An kama Mista Mamu ne a ranar 7 ga watan Satumba bisa zargin hada baki da 'yan ta'adda.

An kama shi ne a kasar Masar a kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajji. Har yanzu dai jami’an ‘yan sandan sirri na tsare da shi bisa zarginsa da aikata laifin.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida