Gayen Ya Hadu: Budurwa Ta Fada Tarkon Son Dan Achaba, Bidiyonta Ya Haddasa Cece-kuce

Gayen Ya Hadu: Budurwa Ta Fada Tarkon Son Dan Achaba, Bidiyonta Ya Haddasa Cece-kuce

  • Wata matashiyar budurwa ta haddasa cece-kuce bayan ta wallafa bidiyon wani dan achaba da kyawunsa ya dauki hankalinta
  • Mutane da dama da suka ga bidiyon sun yi tunanin ko budurwar ta yi wa dan achaban magana tare da karbar lambar wayansa don su ci gaba da magana a gaba
  • Cike da barkwanci, matan TikTok da suka yi martani ga bidiyon sun bukaci budurwar da ta taya su gano inda yake

Wata matashiya yar Najeriya, @olufumi2 ta wallafa bidiyon wani hadadden dan achaba da ya dauko ta daga unguwa.

A bidiyon, budurwar ta dauki kyakkyawan fuskar saurayin jim kadan bayan ta sauka daga achabarsa. Mutumin ya yi kokarin dakewa yayin da yake kallon kamararta.

Budurwa da saurayi
Gayen Ya Hadu: Budurwa Ta Fada Tarkon Son Dan Achaba, Bidiyonta Ya Haddasa Cece-kuce Hoto: TikTok/@olufumi2
Asali: UGC

Budurwa ta nadi bidiyon hadadden dan achaba

Budurwar ta yiwa bidiyon ado da alamar zuciya wanda ke nuna ta fada tarkon soyayyar mutumin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyon sun yi al'ajabin ko ta dauki mataki na gaba da samun lambar wayansa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Bolaji ya ce:

"Wannan mutumin a ado yake na san shi."

lavish01 ta ce:

"Dan achaban na iya kasancewa da kwalin digiri, idan ka tambaye shi."

DaTsAdBoI ta ce:

"Dan achaban Ashewo ne, kalli yadda ya yi da fuska."

LyrIc ta ce:

"Ya fi wasu gayu masu kudi da ke amfani da man bilicin kyau."

angelpiro ya ce:

"Zan fara aiki achaba kwanan nan."

Aluko Gold ta ce:'

"Kamar dai na samu mijin aure dan Allah nemo mun shi."

ayomideogunleye ta ce:

"Gayen na da kyau faaa kudi kawai ya rage. Allah ya albarkace shi."

Ku garzaya Facebook akwai maza aure birjik, wata amarya ta shawarci yan mata yayin da tayi wuff da angonta

Wata budurwa yar Najeriya ta bukaci yan mata da su dunga kula sosai wajen amsa sakonnin tes da ake tura masu ta dandalin zumunta domin a cewarta mazan aure na nan birjik kamar jamfa a Jos a Facebook.

Budurwar dai ta shiga daga ciki ne da wani saurayi da suka hadu a dandalin Facebook tana mai cewa sun tashi daga abokai a shafin zumuntar zuwa abokan rayuwa a zahiri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel