Yan Bindiga: Turo Mu Aka Yi Mu Sace Sanatan Jam'iyyar APC a Neja

Yan Bindiga: Turo Mu Aka Yi Mu Sace Sanatan Jam'iyyar APC a Neja

  • Bayanai sun fara fitowa daga bakin maharan da aka kama sun shiga gidan Sanatan APC a Jihar Neja
  • Wata sanarwa da hukumar yan sandan jihar ta fitar ranar Litinin ta nuna waɗanda ake zargin sun faɗi dalilin zuwa gidan
  • Idan baku manta ba wasu mahara sun shiga gidan Sanata Sani Musa, mai wakiltar Neja ta gabas jim kaɗan bayan ya tafi Abuja

Minna, Niger - 'Yan bindigan da suka shiga a hannu a gidan Sanatan APC, Muhammad Sani Musa, dake Minna, babban birnin jihar Neja sun fara bayanin wanda ya turo su.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kakakin hukumar 'yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Harin yan bindiga.
Yan Bindiga: Turo Mu Aka Yi Mu Sace Sanatan Jam'iyyar APC a Neja Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yaadda Sanata Musa, mai wakiltar mazaɓar Neja ta gabas, wanda ke neman tazarce ya tsallake harin yan bindiga a gidansa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Wani fitaccen sanatan Arewa ya tsallake farmakin 'yan bindiga a gidansa

The Nation ta ce Sanatan ya bar gida zuwa Abuja lokacin da 'yan ta'addan suka barka cikin gidansa a zatonsu yana nan, Allah ya yi taimako aka rutsa aka kama su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wanene ya turo maharan gidan sanatan?

Kakakin yan sandan yace a sabon bayanin da suka yi, waɗanda ake zargi sun ce sun samu labarin Sanatan ya koma jihar Neja ne domin ya halarci bikin naɗi da miƙa sandar mulki ga Sarkin Kagara.

Abiodun ya ƙara da cewa maharan sun ce wani mai suna Sherrif ne ya sanar da su labarin. Sanarwan tace:

"Mun sake samun bayanan gaskiya yayin binciken da muke, ɗaya daga cikin yan bindigan ya amsa laifinsa da cewa ƙarƙashin jagorancin Sharrif, wanda ake nema ruwa a jallo, suka nufi Sanatan a gidansa dake Minna."
"Maharan sun yi tsammanin cewa yana gida saboda ya halarci bikin naɗin Sarauta a Kagara a ranar da suka je da nufin sace shi."

Kara karanta wannan

Iree: An Samu Wasu ‘Yan Iskan Gari Sun Je Fadar Sarki, Sun Banka Masa Wuta

Bugu da ƙari, Abiodun yace maharan sun bincike ko ina a gidan yayin da suka yi ɓadda kamar jami'an tsaro da suka je bincike. Ya kara da cewa dakaru sun bazama don kamo ragowar.

Tashin Hankali Yayin da Wasu ’Yan Bindiga Suka Yi Kokarin Farmakar Sanatan Neja a Gidansa

Tun farko kun ji cewa wasu miyagun yan bindiga sun kai farmaki cikin gidan Sanatan APC a Minna, jihar Neja

Bayanai sun nuna cewa maharan sun kutsa gidan ne da tsammanin yana nan bayan dawowa daga Abuja amma bisa sa'a Allah ya masa gyaɗar dogo har ya kama hanyar koma wa.

Wannan ne karo na biyu da ake kokarin farmakar sanatan, inda a farko aka yi kokarin hallaka shi a gidansa da ke Minna shekaru biyu da suka gabata a salo mai kama da wannan, amma ba a same shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262