Mutum 6 ‘yan Gida 1 Sun Tafi Barzahu Bayan Cin Abincin da Tsaka Ta Fada

Mutum 6 ‘yan Gida 1 Sun Tafi Barzahu Bayan Cin Abincin da Tsaka Ta Fada

  • Mutum shida ‘yan gida daya sun sheka lahira bayan sun ci abincin dare da tsaka ta fada ciki kuma suka kwanta bacci
  • Akwai maigida da matarsa, yaransu biyu sai wasu ‘yan uwansu biyu, duk sun mutu a baccinsu inda daga bisani aka ga tsakar a tukunyar miya
  • Mai gadinsu Lawal Ojo ne yaji shirunsu yayi yawa bayan Gari ya waye, lamarin da yasa ya kira makwabta suka balle kofa tare da ganin gawawwakinsu

Ogun - Mutum shida ‘yan gida daya sun rasa rayukansu bayan sun ci abincin da tsaka ta fada ciki a yankin Mowe dake karamar hukumar Obafemi Owode dake jihar Ogun.

Tsaka ta kashe mutum 6
Mutum 6 ‘yan Gida 1 Sun Tafi Barzahu Bayan Cin Abincin da Tsaka Ta Fada. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Wadanda lamarin ya ritsa dasu sun hada da Adeleke John Samuel, ma’aikacin banki, Pamela Adeleke wacce ita ce matarsa, ‘ya’yansu biyu da ‘yan uwansu biyu.

Kara karanta wannan

Ana Sallar Isha’i, ‘Yan Bindiga Sun Harbe Liman, Sun Tasa Keyar Masu Sallah Babu Adadi a Katsina

An ga gawawwakinsu a sa’o’in farko na ranar Juma’a kamar yadda rahoton jaridar TheCable ya bayyana.

Rahoton ya kara da cewa, an gano mummunan lamarin ne yayin da Lawal Ojo, mai gadinsu, yayi zargin shirun gidan yayi yawa bayan gari ya waye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Yayi wa makwabta magana wadanda suka balle kofar suka shiga amma suka samu gawawwakinsu a dakuna daban-daban.”

- Rahoton yace.

“Dukkansu kwance suke kamar suna bacci, lamarin dake nuna a bacci suka mutu.”

- Majiyar tace.

An gano bakin zaren

Kamar yadda rahoton Ifenatuora Ijeoma, wata ganau ya bayyana, tace zai yuwu gubar ta shiga abincin ne yayin da suke dafa abincin dare.

Ta jaddada cewa, bayan an tsananta duba madafin gidan, an samu tsaka a cikin tukunyar miyarsu.

Bincike kan gubar dake tattare da tsaka

Wani bincike da Afrika Check suka yi a 2018 ya bayyana cewa, tsaka basu da guba. Kwararru sun ce tsaka na dauke da kwayoyin cuta ne masu tarin yawa amma hakan ba zai sa a mutu dole ba bayan an ci abincin da ta fada ciki.

Kara karanta wannan

Bayan Shan Lugude da Gurfana a Kotu, Dalibin da ya Zolaya Aisha Buhari ya Koma Makaranta

Animal Diversity Web kuwa na jami’ar Michigan dake Amurka ya bayyana cewa tsaka basu da guba kuma basu da illa ga ‘dan Adam.

Tsire da ruwan lemo ya kashe mutum 7 ‘yan gida daya

A wani labari na daban, mutane bakwai ‘yan gida daya sun tafi barzahu bayan shagali da suka yi kan tsire da ruwan lemo.

An gano cewa, Mista Jessey, mai gidan ne ya siyo tsiren a garin Umuahia inda iyalansa suka kwashi Gara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng