Aisha Buhari: Yadda Aminu Ya Gana da Wani Gwamnan Arewa Bayan Ganin Buhari Ya Gagara a Villa
- Dalibin da ya soki Aisha Buhari uwargidar shugaban kasa, Aminu Muhammed dai ya koma cikin yan uwansa
- An tsara Aminu zai ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar villa amma dai lamarin ya gagara yiwuwa
- A karshe dalibin na jami'ar tarayya da ke Dutse ya hadu da Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi har ya yankar masa tikitin komawa Jigawa
Bayan sakinsa daga gidan gyara hali, an shirya Aminu Muhammed, dalibin da ya soki Aisha Buhari zai gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kamar yadda wani kawunsa ya bayyana.
A watan Yuni ne dai Aminu wanda ke ajin karshe a jami'ar tarayya ta Dutse ya yi wani rubutu a shafin Twitter cewa uwargidar shugaban kasar ta ci kudin talakawa ta koshi.
Wannan ya yi sandiyar da jami'an tsaro suka kwamushe dalibin sannan suka gurafanar da shi a gaban babbar kotun Abuja mai lamba 14.
Sai dai kuma, uwargidar shugaban kasar ta janye karar da ta shigar kan Aminu a ranar Juma'a bayan matsin lamba daga bangarori daban-daban.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar lauyan mai kara, Fidelis Ogbobe, an janye karar ne bayan manyan yan Najeriya masu fada aji sun saka baki a lamarin.
Aminu bai samu ganin Buhari ba amma sun hadu da Gwamna Atiku Bagudu
A wata hira ta wayar tarho da jaridar Daily Trust, yan uwan Aminu sun nuna farin ciki kan sakinsa da aka yi sannan sun bayyana yadda ziyarar da aka shirya dalibin zai kaiwa shugaban kasa ya balgace.
Kawunsa Shehu Baba Azare wanda ya yi jawabi a madadin dangin ya ce:
"An saki Aminu a jiya (Juma'a) kuma muna ta jiransa saboda mun ji cewa an shirya zai kaiwa shugaban kasa ziyara a fadar shugaban kasa a daren jiya amma abun takaici hakan bai yiwu ba, daga baya suka daga ziyarar zuwa safiya yau (Asabar) amma duk da haka bai yiwu ba. A karshe dai, sun gana da gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu wanda ya daukar masa hayar jirgi daga Abuja zuwa Dutse a Jihar Jigawa inda Aminu ya samu tarba daga abokansa da masu masa fatan alkhairi.
"Gaba daya ahlin na matukar farin ciki da sakinsa saboda muna ta fafutukar ganin ya samu yanci da dadewa. Da farko, mun ga kamar ba za mu iya ba har sai da muka fito da lamarin gaban kotun duniya inda muka samu taimako daga jama'a, kafafen watsa labarai, shugabannin tsaro da kuma daga koina. A karshe Aminu ya samu yanci."
A baya mun ji cewa Aminu ya fito fili ya nuna nadama tare da baiwa uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari hakuri kan laifin da yayi mata.
Asali: Legit.ng