Osun: Dan Takarar Majalisar Tarayya a Inuwar Jam'iyyar PDP Ya Mutu
- Jam'iyyar Peoples Democratic Party watau PDP mai mulki a jihar Osun ta yi rashin daya ɗaga cikin 'yan takarar majalisar tarayya
- Mr. Sola Arabambi, ɗan takara a mazaɓar Irewole/Isokan/Ayedaade karkashin inuwar PDP ya rasu ne ranar Asabar 3 ga watan Disamba
- Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar a PDP, Prince Dotun Babayemi, ya kaɗu da jin labarin rasuwar, ya jajantawa iyalansa da yan uwa
Osun - Mai neman zama ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Irewole/Isokan/Ayedaade a jihar Osun karkashin inuwar PDP, Mista Sola Arabambi, ya riga mu gidan gaskiya.
Wani hadimin marigayi Arabambi, wanda ya nemi a sakaya bayanansa ne ya tabbatar da rasuwar ɗan siyasan, kamar yadda jridar Punch ta ruwaito.
Hadimin ya bayyana cewa uban gidansa ya kwanta dama ne ranar Asabar, 3 ga watan Disamba, 2022 bayan fama da rashin lafiya ta ƙankanin lokaci.
Haka zalika a wata sanarwa daga Ofishin yaɗa labarai na gidan tsohon ɗan takarar gwamnan Osun a inuwar PDP, Prince Dotun Babayemi, yace mutuwar Arabambi ta ɗaga masa hankali.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kuma bayyana marigayin da wani mutum mai kirki kuma wanda ya ɗauki ɗamarar yi wa al'ummarsa aiki dagasken gaske, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Sanarwan ta ce:
"A zahirin gaskiya, mutuwar Sola ta zo mun bagatatan kuma ta kaɗa ni, ya kasance mutum na al'umma."
"Ya taimaki rayuwar mutane da dama da arzikin da Allah ya masa, bisa haka ba za'a taɓa matawa da gudummuwarsa ba."
Mista Babayemi ya kuma miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin, jam'iyyar People Democratic Party watau PDP da kuma ɗaukacin al'ummar mazaɓarsa.
Tsohon ɗan takarar gwamnan ya yi addu'an Allah ga jikan mamacin kana ya baiwa iyalai, yan uwa da abokan arziki hakurin jure wannan babban rashi.
Gwamna Yahaya Bello Ya Ziyarci Nyesom Wika Na Ribas, Sun Sa Labule
A wani labarin kuma Gwamna Yahaya Belle Ya Sa labule da gwamna Wike na jihar Ribas a gidansa na kai da kai dake Patakwal
Gwamna Bello, shugaban matasan kwamitin yaƙin nema zaɓen APC na kasa ya zama na karshe da ya gana da Wike, jagoran tafiyar G5.
Wike, jagoran G5 ya kafa sharaɗin canza shugabancin PDP ta ƙasa kafin ya tallata ɗan takara, Atiku Abubakar.
Asali: Legit.ng