Kwana Hudu da Aure, Amarya Ta Kama Angonta da Yar Uwarta Suna Jin Dadi a Gado

Kwana Hudu da Aure, Amarya Ta Kama Angonta da Yar Uwarta Suna Jin Dadi a Gado

  • Kwana hudu bayan ɗaura musu Aure, wata amarya ta kama Angonta yana saduwa da 'yar uwarta a kan gado
  • Sabuwar amaryar da abun ya sosa wa zuciya, tace lamarin ya taɓa ta yadda ta koma Otal na tsawon mako ɗaya ba wanka da yawo
  • Ta garkame lambobin mahaifiyarta da Surukarta saboda sun nemi ta yafe wa mijin da yar uwarta

Wata mata ta ja hankalin ma'abota shafukan sada zumunta bayan ta tona yadda ta kama Mijinta na holewarsa a gado tare da 'yar uwarta kwanaki huɗu da ɗaura musu aure.

A wani Bidiyo da ta saki a shafin TikTok, Matar tace abinda ta gani wanda bata taɓa tsammani ba ya fasa mata zuciya ta yadda ta killace kanta a dakin Otal tsawon mako ɗaya, ba wanka ba yawo.

Kara karanta wannan

Abu Mai Sosa Zuciya: Hotunan Wani Matashi Bai Ci Abinci Ba Tsawon Kwana 2 ya Samu Taimako

Labarin cin amana.
Kwana Hudu da Aure, Amarya Ta Kama Angonta da Yar Uwarta Suna Jin Dadi a Gado Hoto: @tottie_vision
Asali: UGC

Yayin da ta koma wurin aiki, ta ci karo da Angonta da kuma 'yar uwarta sun zo neman ta yafe musu. Daga baya ta tsoshe lambobinsu.

Ba zata yafe musu ba

Matar ta ƙara da cewa ta toshe lambar mahaifiyarta da kuma lambar Surukarta saboda sun roki ta yafe wa mutanen biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tace daga baya ta tattara kayanta ta koma gidan kawarta. Tace ba mamaki shiyasa 'yar uwarta ta yi shigar fararen kaya a ranar bikin.

A wasu kalamansa, amaryar tace:

"Na shiga yanayi na koma Hotel ba wanka ba yawo na tsawon mako guda. Ranar da na fita aiki dukkansu sun zo neman gafarata. Na tambaye su anya ɗan uwan mijina ne uban yaron nan ɗan shekaru hudu, suka fara inda-inda."
"Na toshe lambobinsu baki ɗaya har da mahaifanmu saboda sun roki na yafe musu. Daga nan na koma gidan hutun ƙawata na kama holewa ta da masoya da zuwa wurare daban-daban."

Kara karanta wannan

"Kaunarsa Take" Wata Mata Ta Nuna Farin Ciki a Bidiyo Lokacin Da Ta Kama Yar Aiki Ta Kwanta da Ɗanta

Duba bidiyon anan

Yadda mutane suka faɗi ra'ayoyinsu

user7673479997905:

"Aikin da kike ne ya cece ki daga shiga matsanancin hali, yar uwarki ta wuce gona da iri, ina miki fatan warwarewa wata rana."

Fun in the bakes yace:

"Ka ci amanata ni kuma na datse alakarmu, ba zan ji tsoron faɗin gaskiya ba. Amma daga karshe zai girbi abinda ya shuka, ni kuma na yi gaba."

A wani labarin kuma Kyakkyawar Budurwa Ta Kashe Aurenta Na Watanni 3, Ta Saki Hotunan Bikinta

Wata matashiyar ‘yar Najeriya mai suna Bolaghold ta haddasa cece- kuce a soshiyal midiya bayan ta bayyana cewa aurenta na watanni uku ya mutu murus.

Matashiyar ta bayyana cewa babu ta yadɗa matsaloli zasu zama masalaha kuma ba dole sai mace da namiji sun yi aure sannan Allah zai basu haihuwa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262