'Yan Bindiga Sun Halaka Mutane 7 Sun Sace Wasu a Sabon Harin Jihar Sakkwato.

'Yan Bindiga Sun Halaka Mutane 7 Sun Sace Wasu a Sabon Harin Jihar Sakkwato.

  • 'Yan fashin dajin sun yi ajalin mutane Bakwai, suka sace wasu biyar a hare-haren da suka kai kauyuka 4 a jihar Sakkwato
  • 'Yan ta'addan sun kai hare-haren ne lokuta daban-daban a garuruwan kananan hukumomi biyu na jihar
  • Shugaban ƙaramar hukumar Goronyo, Abdulwahab Goronyo, ya ce maharan sun tattara dabbobi sun tafi da su

Sokoto - 'Yan bindigan daji sun kashe mutane Bakwai kana suka yi awon gaba da wasu 5 a hare-hare daban-daban da suka kai garuruwa a kananan hukumomin Goronyo da Sabon Birni a jihar Sakkwato.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa garuruwan da aka kai harin sun haɗa da, Bare, Kagara, Kojiyo a yankin Goronyo da kuma kauyen Faji a karamar hukumar Sabon Birni.

Harin 'yan bindiga.
'Yan Bindiga Sun Halaka Mutane 7 Sun Sace Wasu a Sabon Harin Jihar Sakkwato. Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Bayaani sun nuna cewa maharan sun kashe mutane Shida a ƙauyen Bare kuma suka yi ajalin wani bawan Allah a ƙauyen Kagara. Bayan haka yan bindigan sun fasa shaguna sun kwashi kayayyaki.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Jigon PDP a Jihar Arewa, Sun Nemi Fansar Miliyan N100m

Shugaban ƙaramar hukumar Goronyo, Abdulwahab Goronyo, ya tabbatar da faruwar kai hare-haren 'yan ta'adda ƙauyukan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yace maharan sun tattara dabobin gida da yawa sun yi awon gaba da su a ƙauyuka. A bayanansa yace lamarin ya faru ne ranar Laraba da misalin karfe 4:00 na yamma.

A ƙauyen Faji, an ce yan bindigan sun sace mutane biyar cikinsu har da wani Magidanci da matansa biyu. Mutanen sune, Alhaji Yusuf, Suwaiba Isa, Ɗangumi da matansa 2.

Wane mataki jami'an tsaro suka dauka kan lamarin?

Lokacin da aka tuntuɓe shi, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Sakkwato, DSP Sanusi Abubakar, yace rahoton hare-haren bai zo Ofishinsa ba.

Sai dai ya yi alƙawarin tattara bayanai kan lamarin kana ya dawo ga manema labarai amma har yanzun da muke kawo muku wannan rahoton bai yi hakan ba.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wata Matar Aure, Maryam, Ta Sheke Kishiyarta Kan Abu Daya a Arewa

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji Masu Yawa Kan Hanyarsu Na Zuwa Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa wasu matafiyar a Motar Bas mai ɗaukar mutane 18 sun shiga hannun masu garkuwa da mutane a yankin jihar Kogi, zasu je Abuja.

Har yanzun babu caikken bayani kan adadin mutanenda aka sace domin ba'a san ko motar cike take da fasinjoji ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel