Yanzu Yanzu: Buhari Ya Caccaki Gwamnonin Da Ke Taba Kudaden Kananan Hukumomi
- Shugaba Muhammadu Buhari ya caccaki gwamnonin jihohi kan yadda suke ha'intan masu rike da madafun iko a matakin kananan hukumomi
- Buhari ya ce gwamnoni kan zabtare wani kaso daga cikin kudaden shiga da ake warewa kananan hukumomi
- Ya ce irin wadannan abubuwa na kara nuna yadda cin hanci da rashawa suka yi katutu a kasar
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana a ranar Alhamis, 1 ga watan Disamba, cewa gwamnoni na sata daga cikin kudaden da ake warewa kananan hukumomi, Channels TV ta rahoto.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne daga kasan zuciyarsa bayan gabatar da jawabinsa a wajen wani taro da aka shirya ma mambobin da ke daukar manyan kwas na 44 (2022) na hukumar NIPSS a fadar shugaban kasa Abuja.
Yadda gwamnoni ke karbar kudi a madadin kananan hukumomi amma su ki mika duka
Har ila yau, Buhari ya tuna da wani lamari na yadda wani gwamnan jiha zai karbi kudaden shiga a madadin kananan hukumomi a jiharsa, sai kawai ya mika rabin wannan kudi ga shugabannin kananan hukumin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Buhari ya alakanta al'amarin da rashin gaskiya da ke tsakanin yawancin mutanen da ke rike da irin wadannan mukaman.
A cewarsa irin wadannan ayyukan abun kyama ne kuma suna nuna matakin da cin hanci da rashawa ya kai a kasar rahoton The Nation.
Buhari ya daurawa gwamnoni laifin jefa yan Najeriya cikin talauci
A wani labarin kuma, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya daurawa gwamnonin jihohi laifin jefa al'umma cikin kangin talauci saboda sun ki bayar da gudunmawarsu wajen toshe kafar talauci daga tushe.
Karamin ministan kudi, Clem Agba, ya bayyana cewa shirin bayar da tallafi na gwamnati bai yi tasiri ba sosai saboda gwamnoni sun gaza aiki tare da gwamnatin tarayya.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba, 30 ga watan Nuwamba, a Abuja, inda ya zargi gwamnonin da aiwatar da ayyukan bogi maimakon inganta rayuwar mutane a jihohinsu.
Har ila yau, ministan ya ce gwamnonin sun ki amfani da damar albarkar fili da Allah ya yiwa kasar wajen zuba hannun jari a bangaren harkar noma.
Asali: Legit.ng