Ana Tsaka da Shari’ar Aisha Buhari, Matar Tsohon Gwamna ta Kai Korafin Matar Dake Cin Zarafinta a Intanet

Ana Tsaka da Shari’ar Aisha Buhari, Matar Tsohon Gwamna ta Kai Korafin Matar Dake Cin Zarafinta a Intanet

  • Matar tsohon gwamnan jihar Ekiti, Bisi Fayemi, ta kai korafi gaban kwamishinan ‘yan sanda kan wata mata dake cin zarafinta ta yanar gizo
  • A korafin Fayemi, matar ta wallafa cewa an kama ta da N500m na jihar Ekiti a Dubai a 2018 da N710m kwanaki kadan bayan rantsar da mijinta
  • Sai dai a wallafar matar, tace tana lafiya kuma zata baje kolin shaidunta matukar aka gurfanar da ita a gaban kotu don ba kage ko sharri take yi ba

Ekiti - Uwargidan tsohon gwamnan jihar Ekiti, Bisi Fayemi, ta kai korafi ga ‘yan sanda inda take bukatar a binciki wata mata mai suna Abimbola Olajumoke Olawumi, jaridar Daily Trust ta rahoto.

‘Yan sanda
Ana Tsaka da Shari’ar Aisha Buhari, Matar Tsohon Gwamna ta Kai Korafin Matar Dake Cin Zarafinta a Intanet. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A korafin mai kwanan wata 14 ga Nuwamba kuma aka aike shi ga kwamishinan ‘yan sanda ta hannun lauyanta, Mista Luke Ekene Mbam na Octodas Attorney, ta zargi matar da zalintarta ta yanar gizo, bibiya ta yanar gizo da farmaki ta dandalin sada zumuntar zamani.

Korafin Bisi Fayemi

Jaridar TheCable ta rahoto cewa, Fayemi wacce ta yanko tanadin dokokin laifukan yanar gizo na 2015, ta jaddada cewa Abimbola a yayin yada karya a kanta, ta kasa fitowa ta bayyana gamsasshiyar shaida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tace bata da wani zabi da ya wuce ta kai korafi wurin ‘yan sanda domin su wanke sunanta tare da mutuncinta wanda tayi shekaru tana ginawa.

A wallafa masu tarin yawa, Olawumi ta shafinta na Facebook ta zargi Fayemi da kange iyalanta daga kame ko gurfanawar kan laifukan da suka hada da cin zarafi.

Ta kara da zargin matar tsohon gwamnan da wanke kudin sata da suka kai N500 miliyan a Dubai tare da satar N710 miliyan makonni kadan bayan rantsar da mijinta matsayin Gwamna a 2018.

Olawumi tayi martani

Olawumi yayin martani kan korafin a wata wallafa da tayi tace:

“Ku tabbatar, ina nan lafiya.
“Ban girgiza ba ko kadan, saboda zan iya kare kaina kan duk abinda na rubuta a gaban kotu.
“An kama ta da N500 miliyan na kudin Ekiti a Dubai a 2018. Zamu baje shaidar a kotu, jira kawai nake a kira ni.”

Iyayen dalibin da Aisha Buhari ta kama sun rokon yafiya

A wani labari na daban, iyayen Aminu Muhammad, dalibin jami’ar Dutse dake jihar Jigawa, wanda ya ‘zagi’ Aisha Buhari a Twitter sun roki yafiya.

Iyayen Aminu Muhammad sun ce basu san da an kama ‘dansu ba sai bayan kwanaki da ya bace ba a gan shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel