Gwamnatin Jihar Kano Ta Saduda, Ta Janye Dokar Haramta Adaidaita Sahu Kan Wasu Titunan Jihar
- Rahotannin da ke fitowa daga jihar Kano sun bayyana cewa, gwamnati ta saduda, ta cire dokar da ta sanya kan 'yan adaidaita sahu na takaita zirga-zirga
- A makon nan ne hukumar KAROTA ta sanar da haramtawa direbobin adaidaita sahu bin wasu manyan titunan jihar saboda wasu daidai
- Jama'ar jihar, musamman wadanda lamarin ya shafa sun yi korafi, gwamnati ta yi duba ga kokensu ta hakura ta janye dokar gaba daya
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta janye wata dokar da ta sanya kan takaita zirga-zirgar baburan adaidaita sahu a kan wasu titunan jihar.
Baffa Abba Dan'agundi, shugaban hukumar KAROTA a jihar ne ya bayyana hakan a yau Laraba 30 ga watan Nuwamba.
Ya bayyana cewa, dakatarwar ta zama dole duba da yadda 'yan adaidaita sahu suka karbi dokar da aka saka, rahoton Platinum Post.
Ya kuma bayyana cewa, koken jama'a na daya daga cikin dalilan da suka ja gwamnati ta dauki matakin dage dokar, kamar yadda dan asalin jihar Kano, Abba Hikima ya bayyana a shafinsa na Facebook.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda aka dakatar da jigilar adaidaita sahu a wasu manyan titunan Kano
A tun farko, gwamnatin jihar Kano ta bakin KAROTA ta bayyana fito da sabuwar dokar haramtawa 'yan adaidaita bin wasu manyan titunan jihar.
A cewar sanarwar da aka fitar, titunan da aka haramtawa 'yan adaidaita bi sun hada da titin Ahmadu Bello zuwa Mundubawa da titin Tal’udu zuwa Gwarzo, rahoton Channels Tv.
'Yan adaidaita sahu sun bayyana kokensu, inda suka nuna an tauye hakkinsu na sana'a, lamarin da ya jawo cece-kuce a kasar nan.
A gefe guda, hukumar KAROTA ta bayyana daukar mataki kan duk wanda aka kama da saba dokar da gwamnatin ta sanya a makon nan.
Yanzu dai an janye dokar gaba daya.
Direban adaidaita sahu, kuma mazaunin jihar Kano, Muhammad Musa ya zanta da wakilin Legit.ng Hausa, inda ya bayyana jin dadinsa ga wannan doka.
A cewarsa:
"Gwamnati ta yi tunani, domin mun yi koke gareta kuma ta amsa. Daga jiya zuwa yau babu abin da ake magana a kai sai batunmu, amma Allah ya warware komai.
"Sana'ar nan itace komai namu, kuma kan manyan tituna ana samun fasinja masu gwabi, don haka hana mu zai shafi shigar kudinmu.
"Kuma ma ya ake so mutane su yi? Abubuwan da gwamnati ta samar ba lallai ya daure ba, ka san yadda abubuwan gwamnati suke."
Ganduje zai karasa ayyukan tituna da ke kaiwa ga kauyen Kwankwaso
A wani labarin kuma, gwamna Ganduje ya bayyana cewa, zai karasa ayyukan tituna da ke kaiwa ga Kwankwaso a wani yankin jihar ta Kano.
Rahotanni sun bayyana adadin kudaden da gwamnatin ta ware tun farkon shekarar nan domin gudanar da ayyukan.
Sai dai, an ce dole kudin aikin ya karu duba da yadda kayayyaki suka kara farashi a kasuwanni cikin wannan shekarar.
Asali: Legit.ng