Babban Rashi: Tsohon Minista Paul Unongo Ya Rasu Yana da Shekaru 87
- Yanzu muke samun labarin rasuwar daya daga cikin shugabannin Arewa kuma mai fada a ji a zauren dattawan Arewacin Najeriya
- Allah ya yiwa Paul Unongo, wanda tsohon minista ne rasuwa bayan jinya da ya sha fama da ita na tsawon lokaci a Jos
- Najeriya ta ga rashin manyan dattawanta a wannan shekarar, rahotanni sun bayyana wasu jiga-jigan masu fada a ji a kasar nan da suka kwanta dama
Jihar Benue - Wantaregh Paul Unongo, minista a jamhuriyar farko ta Najeriya ya kwanta dama, inji rahoton jaridar Daily Trust.
Unongo, wanda babban jigo ne kuma dattijon kasa a Najeriya ya rasu yana da shekaru 87 a duniya.
Wata majiyar dangi ta shaidawa jaridar a Makurdi, babban jihar Benue cewa, Unongi ya rasu ne a wani asibitin Jos, jihar Filato inda ya yi fama da rashin lafiya.
Ya rike shugabancin zauren dattawan Arewa
Majiyar ta dangi ta kuma bayyana cewa, tsohon ministan wanda shine shugaban zauren dattawan Arewa ya kwanta rashin lafiya na tsawon lokaci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A shekarar 2017 ne Paul ya gaje kujerar Maitama Sule a matsayin shugaban zauren dattawan Arewa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Hakazalika, ya zuwa rasuwar shine shugaban majalisar cigaban ilimi ta Najeriya (NERDC).
Ana kyautata zaton majalisar kabilar Tiv za ta sanar da rasuwarsa kamar yadda majiyar ta bayyana.
An haife shi ne a ranar 26 ga watan Satumban 1935, kuma kasance tsatson Kwaghngise-Anure-Abera a garin Turan na karamar hukumar Kwande ta jihar Benue.
Najeriya na ci gaba da fuskantar dauki dai-dai daga manya kuma jiga-jigan masu fada a ji a kasar.
Allah Ya Yiwa Dan Tsohon Ministan Buhari Rasuwa
A wani labarin, tsohon ministan Buhari, Simon Dalung ya yi rashin dansa a wannan shekarar, kamar yadda rahotanni suka bayyana a watan Oktoban da ta gabata.
Labarin rasuwar Nehemiah Dalung mais shekaru 33 na zuwa ne daga bakin mahaifinsa a shafinsa na Facebook, inda ya ya bayyana shiga jimami da rashin dan nasa.
Ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa:
“Duk da cewar rayuwar Nehemiah ta zo karshe kafin mu shirya mata, ba za mu taba mantawa da rayuwar da yayi da mu ba."
Asali: Legit.ng