Manoma Masu Samar da Kwai Sun Shiga Tsaka Mai Wuya, An Yi Hasashen Abinda Ka Iya Faruwa da Yan Najeriya
- Hasashe sun nuna kwai na iya yin batan dabo a kasuwannin Najeriya yayin da abubuwan yinsu ke kara tsada
- Manoman kwai sun fara karaya da yadda abubuwa ke gudana a yanzu haka musamman ta bangaren tsadar abinci a kasar
- Kungiyar PAN ta yi kira ga gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta fito da hatsi daga rumbun kasa don tallafawa masu kiwon kaji
Yan Najeriya za su kara fuskantar tsadar kwai yayin da manoman kwai ke fama da hauhawan farashin abubuwa. A yanzu farashin kiret din kwai ya kai N2,200.
Tsohon sakataren kungiyar masu kiwon kaji na Najeriya (PAN) reshen jihar Lagas, Olufemi Stephens, ya koka kan yanayin tsadar abincin kaji.
Stephen ya ce manomi kan kashe kimanin N1,800 wajen samar da kwai kiret daya, yana mai cewa hauhawan farashin abincin kaji shine babban matsalar.
A cewarsa, abinci shine ne ke jan kimanin kaso 60-70 cikin dari na farashin kwai.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya yi bayanin cewa farashin abinci shine ke kiyasta yadda za a siyar da kwan, yana mai cewa wasu har kusan asara suke yi.
Manoman kwai na gab da ficewa daga sana'ar
Shugaban kungiyar PAN reshen Akwa Ibom, Solomon Ekong, ya koka cewa hauhawan farashin abincin kaji na tasiri sosai a kan manoma.
Ekong ya ce:
"Farashin abincin kaji ya hau sosai. Farashin da muke bayar da kaji ga masu ci na gida ba zai taba iya yin daidai da abun da muke kashewa wajen samar da su ba. Muna siyan buhun abincin kaji masu kwai kan N7,800. Ba tsayayyen farashi bane, yana chanjawa a kowani lokaci.
“Buhun abincin kananan kaji na ci (broiler) ya kai N13,000. Farashin kaji a ranar da aka kyankyashe su N750 ne zuwa N800. Masu aikin kyankyasan kaji sun fara janyewa saboda ba za su iya ci gaba da tsadar abubuwa ba. A yanzu, masu siyarwar basa samun masu siya a wannan farashin. Da dama sun fara janyewa daga sana’ar.”
Mafita daya ga wannan matsala
Shawarar da ya bayar shine cewa gwamnati ta saki hatsi daga rumbun kasa saboda manoma su rafe farashin abincin kaji, idan ba a haka ba mutane yan kadan da suka rage
Ya jadadda cewar manoma da daman a jiran watan Disamba ya zo su siyar da kajinsu ne saboda ba za su iya jure tsadar abubuwa ba.
Ya ce a matsayinsu na kungiya sun roki manoma da kada su janye domin sun kai kokensu gaban gwamnati, cewa suna fatan rangwame zai iya zuwa daga bangaren gwamnati daga yanzu zuwa shekara mai zuwa.
A cewarsa, gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele, ya sanar da masu kiwon kaji cewa gwamnati za ta saki hatsi.
“Muna sa ran kungiyarmu ta kasa za ta yi hadaka da babban bankin don tabbatar da ganin cewa manoma na gaskiya ne suka amfana daga shirin.”
Martanin wasu manoman kwai
Legit.ng ta tuntubi wasu manoman kwai don jin yadda suke fama da wannan yanayi, inda suka koka matuka, suna masu nuna gajiyawarsu da karaya da lamarin.
Wani manomi mai suna mallam Nura ya ce shi yanzu yana harkar ne kawai don kada ace mutum ya zauna sakakai babu harkokin yi.
A cewarsa yanzu sam babu riba kusan wata ran idan kajin basu samar da kwan yadda ya kamata ba mutum na tashi babu riba koma ya kusan tafka asara.
Ya ce:
"Yanzu buhun Chikun kusan N7,100 ne a da chan kafin abubuwa su tabarbare N3,500 ne cakal, gaskiya na fara karaya, nifa har na fara tunanin siyar da kajina lokacin bikin Kirsimeti."
A bangarensa, Mallam Salisu ya ce a matsayinsa na mai karamin karfi zai bar harkar idan har abubuwa basu daidaita ba.
Mallam Salisu ya ce:
"Akwai yiwuwar iri na mai karamin karfi a harkar kiwon kajin kwai na daina saboda kayan ba sa tabuwa a kasuwa. Za ka siya abinci da tsada, sannan ka zo fama da magani, idan wurin haya ne ka biya, ga maganar lantarki ga kuma ligilar kula dasu, amma duk da haka ka nemi riba ka rasa.
"Tsammaninmu idan kaka ta yi abincin kaji zai sauka kuma ya wadata, sai muka ga sabanin haka, ba mu gane daga ina matsalar take ba; daga manoma ne ko kuma daga kamfanonin da ke samar da abincin kajin.
"Masu sayen kwai ba sa jin dadi, idan muka kai kaya muna kunyar fadin karin kara farashi, amma ya muka iya? Kowa ya san yadda kasar nan take. Fatanmu Allah ya kawo mana saukin rayuwa, ya daidaita mana al'amura."
Dubai kusa: Gwamnatin Najeriya zata kaddamar da kasuwar gwala-gwalai a Kano cikin 2023
A wani labarin kuma, gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayar da tabbacin cewa kasuwar gwala-gwalai na jihar Kano na gab da fara aiki.
Ma'aikatar ma'adinai da karafa da ta ce za a kaddamar da kasuwar kera gwala-gwalan a shekarar 2023, ta ce zata zama cibiyar gwala-gwalai na duniya ta yadda yan kasashen waje za su zo yin siyayya.
Asali: Legit.ng