Tashin Hankali: Amarya Ta Halaka Uwar Gida da Tabarya a Jihar Bauchi

Tashin Hankali: Amarya Ta Halaka Uwar Gida da Tabarya a Jihar Bauchi

  • Yan sanda sun kama wata Maryam Ibrahim Bisa zargin sheke kishiyarta da Taɓarya a jihar Bauchi
  • Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar, SP Wakil, yace Mijin matan biyu ne ya kawo rahoton abinda ya auku
  • Amarya a wurin magidancin tace faɗan ya fara ne bayan mamaciyar ta mata kyautar tsire

Bauchi - Wata matar Aure ta shiga hannun jami'an tsaro bisa zargin halaka kishiyarta da Taɓarya a Bauchi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Wacce ake zargin ta yi amfani da taɓarya ta narkawa uwar gida a wurin mijinsu a kai kuma hakan ya yi ajalinta.

A cewar hukumar 'yan sanda lamarin ya faru ne a ƙauyen Gar dake yankin gundumar Pali, ƙaramar hukumar Alkaleri, jihar Bauchi.

Maryam Ibrahim.
Tashin Hankali: Amarya Ta Halaka Uwar Gida da Tabarya a Jihar Bauchi Hoto: Punchng
Asali: UGC

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Ahmed Wakil, wanda ya bayyana haka a wata sanarwa yace mijin ne ya kai rahoton abinda ya auku Caji Ofis ɗin Maina-Maji.

Kara karanta wannan

Bauchi: Amarya Ta Ragargaza Uwargidan Har Lahira da Tabarya a Kan Tsire

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

SP Wakil yace:

"Ranar 22 ga watan Nuwamba wani Magidanci, Ibrahim Sambo daga kauyen Gar, yankin Alkaleri ya kai rahoto Hedkwatar Maina-Maji cewa matarsa ta biyu amarya, Maryam Ibrahim, ta narka wa uwar gida Hafsat taɓarya."
"Hafsat Ibrahim ta samu raunuka sakamakon haka, lamarin da ya sa aka kaita Asibitin garin inda Likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa. Bayan samun rahoton Dakaru suka je suka cafke wacce ake zargi."

Me ya haddasa faɗa tsakaninsu?

Kakakin yan sandan ya ƙara da cewa matar ta amsa laifinta, inda ta bayyana yadda abun ya faru da cewa:

"Ranar Talata da abun ya faru, marigayya Hafsan ta aiko ɗanta ya kawo mun Tsire. Bayan taci naman sai ta fara jin ba daɗi har ta amayar da shi. Ganin haka ta kira matar ƙanin mijinsu, Fa'iza ta faɗa mata abinda ya faru."

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Kara Fitowa, Jami'ar FUD Ta Yi Magana Kan Kama Ɗalibinta Da Ya 'Zagi' Aisha Buhari a Twitter

"Tace Faiza ta gaya mata mai yuwuwa Ulcer ce zata taso mata don haka ta ɗauko mata maganin Ulcer. Bayan haka ne wacce ake zargi ta shiga ɗakin girki ta ɗauko Taɓarya ta wuce ɗakin Kishiyar ta buga mata a kai, sanadin mutuwarta kenan."

A wani labarin kuma Wani magidanci garzaya Kotu yana rokon Alkali ya cece shi ya raba shi da matarsa domin tana yunkurin halaka shi

Mista Nnadi Onu, ma'aikacin gwamnati a birnin tarayya Abuja ya bukaci Kotu ta amince da bukatarsa domin babu sauran yarda da aminci a tsakaninsu.

Bugu da ƙari ya faɗa wa Alkalin Kotun cewa matarsa bata ganin girmansa, ga rashin son zaman lafiya, a cewarsa ta kan zo har Ofis ɗinsa ta ci masa mutunci ta kama gabanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262