Gobara ta Lakume Ajujuwa 14, Ofisoshi 12 da Bandakuna 21 a Makarantar Kano
- Gobara ta tashi a Tsangaya Model Boarding School dake kauyen Kiyawa ta karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano inda tayi gagarumar barna
- Ya lamushe ajujuwan karatun dalibai 14, ofisoshin shugabannin makarantar 12 tare da bandakuna 21 dake makarantar
- Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Kano ya tabbatar da cewa gobarar ta fara wurin karfe 1:05 na tsakar ranar Lahadi
Kano - Mummunar gobara a ranar Lahadi ta lamushe shaguna 14, rukunin ofisoshin shugabannin makaranta da bandakuna a Tsangaya Model Boarding School dake kauyen Kiyawa na karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano.
Daily Trust ta rahoto cewa, wannan na kunshe a takardar da kakakin rundunar hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar.
Yace lamarin ya faru a ranar Lahadi da tsakar rana.
“Mun samu kiran gaggawa wurin karfe 1:05 na ranar Lahadi daga Honarabul Ghaddafi Sani Bagwai kuma da gaggawa muka tura tawagar ceto zuwa wurin inda suka isa daidai karfe 1:30 na rana domin hana wutar zuwa sassan makarantar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Kasan bene da ya kai girman taku 400 a tsayi da taku 400 a fadi wanda ake amfani da shi matsayin makarantar kwana ta tsangaya, ajujuwa 14, ofisoshi 12 na shugabannin makarantar duk ya kone kurmus.”
- Yace.
Yace gobarar ta fara ne daga wutar lantarki mai amfani da hasken rana wacce ke ofisoshin shugabannin makarantar.
Gobara ta tashi a kasuwar Singr dake Kano
A wani labari na daban, wata mummunar gobara ta tashi a fitacciyar Singer wacce ake siyar da nau’ikan kayan abinci a Sabon Gari dake jihar Kano.
Gobarar ta fara da lakume wasu daga cikin rukunin shagunan jama’a inda ta ci hatsin miloyoyin Naira wadanda aka adana a dakunan ajiyar ‘yan kasuwa.
An yi gobarar ne a ranar Talata, 15 ga watan Nuwamban 2022 wacce har yanzu ba za a ce ga musabbabin faruwarta ba.
Wasu daga cikin ‘yan kasuwar suna zargin wutar lantarki ce ta assasa gobarar.
Kasuwar Singer dake Kano tayi shuhura wurin siyar da kayan abinci na sari wadanda suka hada da masara, shinkafa, taliya, madar, gero, dawa da sauran nau’ikan kayan abincin da Hausawa ke amfani da su a arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng