Gwamnatin Tarayya Ta Sauya Ranar Dawowar Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja

Gwamnatin Tarayya Ta Sauya Ranar Dawowar Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja

  • Gwamnatin tarayya ta tsawaita ranar dawowar zirga-zirgan jirgin ƙasa a layin dogon Kaduna zuwa Abuja
  • Ministan Sufuri, Mu'azu Sambo, wanda ya sanar da haka a Kaduna, Bai fadi ainihin ranar da jirgin zai ci gaba da aiki ba
  • FG ta dakatar da jigilar jirgin kasa a hanyar ne watanni Takwas da suka wuce bayan 'yan ta'adda sun kai farmaki

Abuja - Gwamnatin tarayyan Najeriya ta hannun ma'aikatar Sufuri ta sanar da ƙara wa'adin dawowar harkokin zirga-zirgan jiragen ƙasa daga Kaduna zuwa Abuja.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Ministan Sufuri, Muazu Sambo, ne ya bayyana haka ga manema labarai a birnin Kaduna ranar Lahadi.

Jirgin ƙasa.
Gwamnatin Tarayya Ta Sauya Ranar Dawowar Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Ministan ya ziyarci Kaduna ne domin gane wa idonsa da duba yanayin da Titin jirgin ƙasa yake ciki yayin da ma'aikatarsa ke shirye-shiryen ci gaba da jigila.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Babbar Mota Ta Murkushe Motocin Ayarin Gwamnan Arewa, Ya Sha Da Kyar

Sai dai a jawabinsa, Ministan bai ambaci ranar da Jirgin zai ci gaba da zirga-zirga a hanyar ba amma ya bayyana cewa ƙarin da za'a samu ba zai wuce mako ɗaya ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Sambo, gwamnatin tarayya ta kirkiro sabuwar hanyar siyan Tikiti, wanda a kalamansa zai zama hanyar farko na fara binciken tsaro ga Fasinjoji.

Mista Sambo yace hakan zai ba gwamnati cikakkiyar damar sanin waye ya shiga jirgin kuma a ina sannan a dai-dai wane lokaci.

Legit.ng Hausa ta gano cewa a makon da ya gabata ne, FG ta sanar cewa a ranar 28 ga watan Nuwamba, 2022 harkokin jirgin ƙasa a titin Kaduna-Abuja zasu dawo.

Meyasa aka dakatar da ayyukan jirgin kasa a Kaduna-Abuja?

Gwamnati ta dakatar da ayyukan jirgin kasan Kaduna-Abuja watanni Takwas da suka shuɗe lokacin da 'yan ta'adda suka dasa Bam suka tashi wani sashin jirgin yana gab da isa tashar Kaduna.

Kara karanta wannan

Minista ya fadi babban abin da Buhari ya yi da 'yan Najeriya za su ke tunawa kullum

'Yan ta'addan sun kashe mutane Shida sannan suka yi awon gaba da wasu Fasinjoji 60, waɗanda zuwa yanzun duk sun shaki iskar 'yanci, kamar yaddda Vanguard ta ruwaito.

A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya tace ta gama bincike kan harin da 'yan ta'adda suka kai gidan gyaran halin Kuje, Abuja

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, yace kundin abubuwan da aka gano a binciken abu ne na tsaro ba zasu bayyana wa duniya ba.

A cewar ministan gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta taka rawar a zo a gani a yaki da mayakan kungiyar Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262