Kada Mu Ji Wani Malami Yana Kamfe A Masallaci, Hukumar INEC Ta Sanar
- Hukumar INEC mai shirya zabe ta saki jerin dokokin yakin neman zaben shugaban kasa, gwamna da yan majalisa
- Yan siyasa masu neman kujerun mulki daban-daban sun kaddamar da yakin neman zabe gadan-gadan
- A ranar Alhamis jirgin yakin neman zaben APC ya garzaya Ebonyi yayinda na PDP ya shirga Ilori
Abuja - Yayinda ake saura watanni uku zaben 2023, hukumar gudanar da zaben kasa mai zaman kanta, INEC, ta fitar da jerin dokokin yakin neman zabe ga jam'iyyun siyasa da daukacin jama'a.
A takardar mai shafi shida da INEC ta fitar, ta haramta zage-zagen juna da tsokanar fada a wajen kamfe kuma an hana tallata wani dan takara a wuraren Ibada, rahoton Channels.
Hakazalika hukumar ta kara da cewa jami'an tsaro kadai aka hallatawa rike makami wajen taron kamfe.
Zaben 2023: Tinubu, Atiku, Obi, Da Wasu Suna Cikin Matsala Yayin Da INEC Ta Fitar Da Sabbin Ka'idoji
A cewar INEC, wadanda aka amince su rike bindige sune yan sanda ko mambobin hukumomin tsaro da aka tura wajen kamfen musamman.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ka jerin dokokin inji INEC:
- "Kada ayi kamfe a cibiyoyin Ibada, ofishohin yan sanda da ofishohin gwamnati."
- "Kada a yi amfani da kalaman batanci kan juna wajen yakin neman zabe."
- "Kada wani dan takara ko jam'iyyu su yi amfani da ofishohin gwamnati ko da na jarida ne"
INEC tace manufar tarukan kamfe shine baiwa yan takara daman sanar da al'umma manufofinsu da abubuwan da suke shirya yiwa mutane.
Hukumar ta bukaci dukkan jam'iyyun siyasa su aikewa mata da wasikar niyyar yakin neman zabe tare da jerin mambobin kwamitin shirya kamfen da kuma izinin yan sanda a jihar da zasu yi.
INEC ta a aike mata da wannan wasika tun ana saura kwanaki goma da ranar da ake niyyar yin kamfen.
Wai Sau Nawa Atiku Zai Yi Takara Ne? Ku Fada Masa Yaje Ya Huta: Tinubu Ya Dira Dan takaran PDP
Dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya caccaki abokan hamayyarsa ranar Juma'a, 25 ga Nuwamba, 2022.
Tinubu ya basu shawaran su janye daga takara saboda shi kadai ne ya cancanci zama shugaban kasa.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin kamfen da ya je masarautar Gbaramatu dake karamar hukumar Warri dake jihar Delta
Asali: Legit.ng