Miji Da Mata Sun Yi Garkuwa Da Maigidansu, Sun Kasheshi Bayan Karban N15m
- An damke Mata da Miji masu garkuwa da mutane a jihar Ogun kuma su kashe wanda suka sace bayan karban kudin fansa
- Shekaru biyu da suka gabata suka kashe maigidan matarsa bayan karban naira milyan 15 hannun yan'uwansa
- Dubunsu ya cika yanzu yayinda suke shirin garkuwa da matar margayin tare da 'dansa
Abeokuta - Jami'an yan sanda a jihar Ogun sun damke Miji da Matarsa da wani abokinsu kan zargin kashe wani attajiri kuma mammalakin Rolak Hotel, Otunba Abayomi Ajayi Smith.
Mijin mai suna Larry Adebayo Adewumi da matarsa mai suna Okereke Olufunmilayo tare da wani Adebowale Sanni sun hallaka attajirin bayan karban kudin fansan N15m daga hannun iyalinsa.
Sun aikata wannan aika-aika tun Satumban 2020 a Anifowose Estate dake Igbeba, Ijebu Ode amma sai yanzu asirinsu ya tonu, rahoton SaharaReporters.
Bayan shekara biyu da kashe attajirin, a Satumban 2022 suka sake kitsa yadda zasu yi garkuwa da matarsa da 'yayansa, hukumar yan sandan jihar ta bayyana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tace:
"A Satumba, rundunar SP Taiwo Opadiran sun samu labarin ana sake shirin garkuwa da matar marigayi Ajayi Smith da yaransa."
"Bincike ya kai ga damke wani Adebowale Sanni a Ikeji Arakeji dake jihar Osun. Ya tona asirin yadda suke bibiyar matar marigayin, Yeye Olusola Roseline Ajayi Smith."
"Ya bayyana cewa Marry ne ya basu bayanan inda dakin Otal dinsu yake da kuma umurnin cewa idan suka samu nasarar sace matar da yaron su kashesu bayan karban kudin fansa kamar yadda suka yiwa mijin shekaru biyu da suka gabata."
An kama mata da mijin
Hukumar ta kara da cewa hakan ya sa suka kai simame damke Larry da matarsa.
Tace:
"Bincike ya nuna cewa Larry dan damfara ne amma ya koma garkuwa da mutane. Ya samu bayanan Otunba Ajayi Smith daga wajen matarsa Olufunmilayo wacce ke yiwa attajirin aiki."
"Larry na da asusun banki biyu inda yake ajiye kudaden fansa. A asusun farko mai lamba 0010913206 dake bankin Jaiz, yana da milyan N34,953,455, yayinda aka samu milyan hudu (N4,576,846) a wani asusun na Access Bank."
Kwamishanan yan sandan jihar CP Lanre. S. Bankole, ya jinjinawa jami'ansa bisa wannan nasara kuma ya umurcesu su binciko sauran mambobin gungun.
Asali: Legit.ng