Fasto Ya Ja Kaya: Wani Shugaban Majami'a Ya Dirkawa Mambobinsa Mata 20 Ciki

Fasto Ya Ja Kaya: Wani Shugaban Majami'a Ya Dirkawa Mambobinsa Mata 20 Ciki

  • Wani shugaban majami'ar Kiristoci ya yi abun ban mamaki a jihar Enugu, kudu maso gabashin Najeriya
  • Babban Faston ya dirkawa mambobin cocinsa mata akalla mutum guda 20 juna biyu lokaci guda
  • Hukumomin sun cika hannu dashi kuma dalilin da ya bada na aikata hakan na da ban mamaki

Wani Fasto mai suna, Timothy Ngwu, shugaban majami'ar Vineyard Ministry of the Holy Trinity dake jihar Enugu ya aikata aika-aikata da matan jama'a a jihar.

Faston mai shekaru 53 a duniya ya dirkawa mambobinsa mata ashirin (20) ciki kuma yace wahayi akayi masa yayi hakan, rahoton Rivers Mirror.

Faston yanzu haka yana garkame hannun jami'ar hukumar yan sandan jihar Enugu.

Fasto
Fasto Ya Ja Kaya: Wani Shugaban Majami'a Ya Dirkawa Mambobinsa Mata 20 Ciki Hoto: Rivers Mirror
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yadda Matar Aure Ta Soki Mijinta Da Wuka Har Lahira Kan Ya Nemi Hada Shimfida Da Ita

Faston ya bayyana dalilin yin hakan yayinda yan sanda suka damkeshi

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Ebere Amaraizu, ya bayyana cewa ana tuhumar Faston da cin zarafin mata.

A cewarsa:

"Faston na ikirarin cewa umurni ya samu daga wajen ubangijinsa. wanda shine ya yiwa duk yarinyar da ruhi mai tsarki ya zaba ciki, ko budurwa ce ko matar aure."

A cewar PMNews, matar Fasto cewa ta kai kararsa wajen yan sanda bayan dirkawa kanwarta ciki duk da sunan samun wahayi.

Fasto mai mata biyar da 'yaya 13 ya karyata zargin da matarsa ke yi masa.

Ya ce bai taba jima'i da kowace yarinya cikinsu ba tare da izinin mazajensu ba.

Rikici: An tasa keyar fasto zuwa magarkama bayan cinye kudin wata malamar makaranta

An damke wani fasto mai suna Raymond Akala Ayodele mai shekaru 36 kuma gurfanar dashi a gaban kotu bisa zargin damfarar wata malamar makaranta N3m.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Dauka Shatar Jirgi Kacoka, Ya Kai Soja Mai Rauni Asibitin Abuja

Matar mai suna, Mrs Omowumi Arowosegbe, na da zama ne a Ikorodu a jihar Legas.

Ayodele shine babban manajan kamfanin ERIIFEi Divine Global Enterprise kuma babban Malamin coci ne shi.

Jami'an sashe na 2 na rundunar 'yan sandan jihar Legas sun damke shi, a cewar PM News.

A cewar 'yan sanda, Ayodele, wanda kuma ya yi ikrarin shi tsohon ma'aikacin Friesland Capena ne da ke Ogba a Legas, ana zargin ya karbi kudade daga matar da sunan zai yi kasuwanci da kudin kana su raba riba.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida