Abinda 'Yan Najeriya Ke Cewa Kan Sabon Kudin Naira da Shugaba Buhari Ya Kaddamar

Abinda 'Yan Najeriya Ke Cewa Kan Sabon Kudin Naira da Shugaba Buhari Ya Kaddamar

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sumfurin kudin naira sabbi da za a fara kashewa a kasar
  • Al'ummar Najeriya sun tofa albarkacin bakunansu a kan wannan sabon kudi inda da dama suka yi addu'an Allah yasa ya zamo silar arzikin kasar
  • Wasu na ganin babu wani banbanci tsakanin sabon kudin da na da cewa kala kawai aka chanja masa

Abuja - A safiyar yau Laraba, 23 ga watan Nuwamba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin takardun naira.

An baje kolin takardun sabbin kudin da suka hada da N1,000, N500 da N200 a wajen wani biki da ke gudana a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Buhari ya kaddamar da sabon kudi
Abinda 'Yan Najeriya Ke Cewa Kan Sabon Kudin Naira da Shugaba Buhari Ya Kaddamar Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Kamar yadda babban bakin CBN ya sanar, zai saki kudaden ne ga jama’a a ranar 15 ga watan Disamba domin su fara amfani da ita.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shin Atiku Zai Yi Sulhu Da Boko Haram? Ɗan Takarar Na PDP Ya Bayyana Abinda Ke Zuciyarsa

Hakazilika, tsoffin takardun naira za su daina amfani daga ranar 31 ga watan Janairun 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jama’a sun yi martani akan sabbin takardun kudi da gwamnatin Najeriya ta saki

Tuni dai al’ummar kasar suka fara tofa albarkacin bakunansu a kan wannan sabon kudi da gwamnatin shugaba Buhari ta saki.

Yayin da mutane da dama suka yi addu’an Allah yasa hakan ya zamo alkhairi da kuma silar farfadowar darajar kudin kasar, wasu na ganin kalar kudin bai yi saboda gane jabunsu zai yi wuya.

Legit.ng ta tattaro martanin wasu daga cikin mabiya shafinta na Facebook a kasa:

Zakariyya Gambo ya yi martani:

“ALLAH ya sa anyi a saa allah ya karamana arziki mai albarka a kasarnantamu.”

Tukur Lawan ya ce:

“Saukin masarufi muke bukata ba canjin kudi ba.”

Mustapha Maulud Dwn ya ce:

Kara karanta wannan

Shugabbanin Kudu Sun Koka Kan Yadda Aka Maida su saniyar Ware Musamman A Faggen Shugabancin

“Allah Ya sa sabbin kudin su zama silar farfadowar darajar Naira a idon duniya.”

Uthman Abdussamad ya yi martani:

“Wadannan din ma wallh saimun kwashe su muje mun boye, don kùma san da sani garama a bugasu dayawa, ni kadai ṣáínà boye fiyeda dubu ashirin wllh.”

Anas Ismail Sdn ya ce:

“Duk mai tsohon kuɗi ya nemi kayan tiri ya tira kuɗin sa har sai sun dawo irin wannan.”

Abdullahi Malah ya rubuta:

“tofah Allha yakyauta Ammafa ni Anawa ganin gaskiya Akwai Ayar tambaya wannan sabon dubudaya launinshi Babu chanjin kirki tsakaninshi datsofo Ina tsoron kada wasu mugayen mutane suke chutar mutane kauye ba lallebane suiya bambanta tsoho da sabon domin launin kisan dayane toh Allha ya. Kyuta.”

Han Ny Ijanada ya ce:

"Kundin bogi zaifi zagaya fiyeda asali domin wannan kalar zai yi wuya mutum ya gane jabun kudi.”

Muhammad HB Yuseef ya ce:

“Nifa Akan Nasa irin Wanga Kudin A Aljihuna Na gwammace Na zauna ba Ko sisi kudin beminba Eheeee,”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya Ta Juyo Kan Manyan Masu Kudi, Tana So a Lafta Masu Haraji

Ukasha Gwandou ya ce:

“Na da sunfimin kyau don haka Ni dasu zan cigaba da amfani ba ruwana da wannan Shirme.”

Hayatu Hammajam ya ce:

“Masha Allah, Allah yabamu alhetin da arzikin amfani da wadata da wannan sabon kudin Aameeeeen.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng