Sheikh Gumi ya Magantu Kan Hakar Man Fetur Karo na Farko a Arewacin Najeriya
- Babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana farin cikinsa bayan hakar man fetur na farko a arewacin Najeriya
- A wallafar da mazaunin Kadunan yayi, ya tabbatar da cewa arziki na tafe yankin arewacin Najeriya nan babu dadewa da izinin Allah
- Gumi yayi kira ga ‘yan Najeriya da su kasance a daidaice don Sokoto River Basin yake fatan ya zama rijiyar man fetur ta gaba da za a fara hakowa
Bayan kaddamar da hakar man fetur na farko a iyakar jihohin Bauchi da Gombe, fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, yayi kira ga ‘yan arewa da su tsayu tare da daidaituwa don arziki na zuwa arewa.
A martaninsa na farko kan hakar man fetur din a arewa da yayi shi ta shafinsa na Facebook a ranar Talata, Sheikh Gumi yace Sokoto River Basin ce zata zama ta gaba wurin hakar man fetur din.
Gumi yace:
“Man fetur na farko a arewa! Ku tsayu a hanya madaidaiciya, arziki na zuwa da izinin Allah! Sauran Sokoto River Basin wurin hakar mai na gaba da izinin Allah.”
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
- Malamin yace.
An kafa tarihi a arewacin Najeriya
A ranar Talata, 22 ga watan Nuwamban 2022 ne aka kafa tarihin hako kan fetur karo na farko a arewacin Najeriya.
An samu nan fetur din a iyakar jihohin Bauchi da Gombe wanda aka sanyawa suna da Kolmani .
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da hakar man fetur din yayin da ya samu rakiyar manyan ‘yan siyasa a fadin Najeriya.
Daga cikin wadanda suka halarci wurin akwai Ministan sadarwa da tattalin arziki mai dogaro da fasahar zamani, Sheikh Isah Ali Pantami, ‘Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu.
Hadimi na musamman ga shugaban kasa a fannin yada labarai, Bashir Ahmad, ya halarci wurin inda hotonsa ya bayyana tare da Sheikh Pantami a safiyar Talata.
Bai tsaya nan ba, ya wallafa hotunan samfurin nan fetur na farko da aka hako daga yankin tare da injina kala-kala da aka kafa domin aikin.
Asali: Legit.ng