Matashi Ya Lashe Gasa Cin Suya A Jihar Legas, Ya Samu Kyautar N250,000
- Wani jarumin maza ya lashe gasar cin tsire mai yaji a jihar Legas kuma ya samu kyautar kudi
- Akalla mutum Talatin wannan matashi ya kayar saboda tsananin zafin nama wajen cin nama
- Kamfanin ya bayyana cewa sama da mutum 700 suka nemi musharaka a wannan gasar
Legas - Wani matashi dan shekara 28, Caleb Otagba, a ranar Lahadi ya zama zakara a gasar cin Suya, karon farko a tarihin a Najeriya.
Caleb, ya samu kyautar N250,000 a gasar da ya gudana a birnin Ikko, jihar Legas.
Kamfanin Sooya Bristo tare da hadin kan Lost In Lagos ne suka shirya gasar domin murnar ranar bude Sooya Bristo, reshen Lekki.
Sama da mutum 30 ne suka yi musharaka a gasar, rahoton NAN.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Caleb, wanda ma'aikaci ne a kamfanin PCV Cleaning Service ya bayyana farin cikinsa bisa wannan nasara da ya samu.
A cewarsa:
"Wannan ne karo na biyu a shekarar nan da zan samu irin wannan nasara, na farko na lashe gasa cin Burger da Lost In Lagos ya shiya, kuma ina godewa Allah tare da sa ran wani nasara kafin karshen shekara."
"Na mayen abinci ne kuma na gano ina kuzarin da nike da shi wajen gasar cin abinci."
Mu'assasar Sooya Bristo, Olamidun Ogundoyin, ta bayyana cewa an shirya gasar ne domin farantawa mutane rai, musamman matasa.
Ita kuwa Manajar Sooya Bristo, Victoria Agorye, ta bayyana cewa sama da mutum 700 suka nemi musharaka a gasar kuma kamfanin ya ji dadin haka sosai.
Victoria ta ce Suya abu mai kyau ne ga jikin dan Adam idan aka gasa cikin tsafta kuma yadda ya kamata.
Cin Suya, Balango, tsire, na kawo ciwon daji, Ku daina ci Likita
A wani labarin kuwa, Wani Likita mai ilmin kiwon lafiya, Dr. Chinonso Egemba, ya gargadi yan Najeriya kan cin namar Suya da bai gas sosai ba asaboda hakan kan haifar da citar Daji (Kansa).
Likitan wanda aka fi sani da ‘Aproko Doctor’ a kafafen ra'ayi da sada zumunta ya yi bayanin cewa akwai sinadarin kemikal dake hawa kan nama irin aka gasa kan hayaki
Ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafinsa na Instagram @aproko_doctor
Asali: Legit.ng