Attajirin Dan Najeriya Ya Shiga Makaranta Da Motar Sama Da Miliyan 24, Dalibai Sun Zagaye Shi
- Wani matashi dan Najeriya ya ja hankalin dalibai da dama lokacin da ya tuka motarsa kirar 2021 CLA 45 AMG zuwa cikin jami’ar Lagas
- Dalibai da dama wadanda suka sha mamakin ganin tsadaddiyar motar sun isa gabanta domin su taba su ji
- Yan Najeriya da dama sun tofa albarkacin bakunansu inda wasu suka yi mamakin dalilin da zai sa shi shiga irin wannan kasaitacciyar mota ta jan hankali
Lagos - Wani matashi dan Najeriya mai suna @habbyfx, ya haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya bayan ya wallafa wani bidiyo da ke nuna lokacin da ya tuka motarsa kirar 2021 CLA 45 AMG zuwa cikin jami’ar Lagas.
Yayin da yake zaune cikin tsadaddiyar motarsa, dalibai da dama sun kewayeta inda suka dungi taba motar tare da nuna sha’awarsu ga wadatar da Allah ya yiwa matashin.
Hakazalika akwai jami’an tsaro kewaye da motar suna kokarin daidaita yanayin. Mutane da dama na ta kokarin cinkar farashin motar.
A cewar Mbusa, farashin motar ta fara daga $55,900 (N24,744,694.00) kuma da hannu aka tsara jikinta. Tana daukar fasinjoji biyar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kalli bidiyon a kasa:
Jama’a sun yi martani
A daidai lokacin wannan rubutun, bidiyon ya tara martani fiye da 500 da kuma ‘likes’ fiye da 44,000.
Legit.ng ta tattara wasu daga cikin martanin a kasa:
CHIDEX ya ce:
“Daukacin gayun da ke taba ta suna fadi a ransu Allah kayi mun irin haka.”
nuel ekeh ya ce:
“Wasu mutane a nan, tafin hannunsu garza ne… da zaran sun taba motar…kwajire ta zasu yi.”
Brooklyn85 ya yi mamaki:
“Dan Allah me ke faruwa a nan, Yesu ne a cikin motar?”
Labbie_mi ta ce:
“Dole ne zai ka kai wannan makaranta, wasu gayun basa son rayuwa mai sauki ko kadan, shior.”
its_Otunba ya ce:
“Wa ya lura murfin wajen zuba main a budewa saboda wani ya yi kusa da shi sosai. Turawa.”
destin11w ya ce:
“Babu yadda za a yin a dauki irin wannan zuwa makaranta ba zan taba ba.”
Knowstalgik ya ce:
“Bayan duk abun da aka ce da yi, mota ce dai. Lol, me yasa mutane ke shafata sai kace it ace mai cetonsu.”
Asali: Legit.ng