Ni Ba Musulmi Bane, Ba Kirista Bane Kuma Bana Bautar Gunki, Soyinka
- Shahararren marubuci, Farfesa Wole Soyinya ya ce gumaka ne abokan tafiyarsa a duk lokacin da ya yi balaguro imma a zahiri ko a tunaninsa
- Babban marubucin ya ce sam babu abun da ya hada shi da addinan kiristanci, musulunci ko na gargajiya sabanin hasashen da wasu da dama ke yi
- Farfersan ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi a wajen wani taro da aka shirya masa
Lagos – Fitaccen marubucin nan na Najeriya, Farfesa Wole Soyinka ya bayyana cewa shi ba Kirista bane, ba Musulmi ba kuma ba dan addinin gargajiya bane.
PM News ta rahoto cewa Soyinka ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Nuwamba, a wajen gabatar da wasu kasidunsa.
An gudanar da taron da aka shirya na musamman domin shi a cibiyar Mike Adenuga da ke Ikoyi, jihar Legas.
Soyinka na amsa wata tambaya da aka yi masa game da addininsa ne a zauren tambaya da amsoshinsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Addinin Soyinka ya bayyana
Babban marubuci ya ce babu ruwansa da addinin kiristanci, Musulunci ko bautar gumaka wato addinin gargajiya, sannan cewa bai taba ji a ransa akwai bukatar ya bautawa wani ba.
Ya ce shi babu wani abun bauta da yake bautawa kuma yana kallon gumaka a matsayin zahirin gaskiya, don haka, sune abokan tafiyarsa a duk lokacin da yayi balaguro imma a zahiri ko a badini
Soyinka yace:
"Ina bukatar addini ne? ban taba ji a raina ina bukata ba, ni masanin tarihi ne. Na yi imanin cewa mutane na da dama kuma ba zasu taimaka wurin hada labarai a kewayensu ba game da abinda suka gani ko suka sa a zukatansu."
Bayani: Abin Da Ya Kamata Kowane Ɗan Najeriya Ya Sani Game Da Harrufan Larabci A Sabbin Takardun Naira
Ya ci gaba da cewa:
“Amma addini? A’a bana bautawa kowani abun bauta. Amma ina kallon gumaka a matsayin zahiri kuma saboda haka sune abokan tafiyata a zahiri da badini.”
Za ku dandana kudarku idan kuka zabi wanin Peter Obi, Jigon siyasa ga yan Najeriya
A wani labari na daban, wani jigon siyasan Najeriya ya shawarci yan Najeriya da su zabi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi a zaben 2023 ko kuma su dandana kudarsu.
Cif Charles Udeogaranya ya ce al'umar kasar za su ci karo da bakar wahala idan har suka yarda suka zabi wanin Peter Obi.
Asali: Legit.ng