Gayu Gudu Na Suke Saboda Ni Kurma Ce, Tsaleliyar Budurwa Ta Koka a Bidiyo

Gayu Gudu Na Suke Saboda Ni Kurma Ce, Tsaleliyar Budurwa Ta Koka a Bidiyo

  • Wata kyakkyawar budurwa mai amfani da TikTok ta bayyana a bidiyo cewa ta rasa tsayayyen saurayi da zai sota saboda nakasar da Allah yayi mata
  • Kyakkyawar matashiyar ta ce da zaran namiji ya fito ya ce yana sonta sai ya tsere idan ya gano cewa ita din kurma ce
  • Mutane da dama da suka kalli bidiyonta sun karfafa mata gwiwar cewa Ubangiji zai kawo mata wanda zai sota tsakani da Allah

Wata kyakkyawar matashiyar budurwa mai suna @allthingssimsim, ta je dandalin TikTok don yin bidiyo tare da sanar da mutane dalilin da yasa har yanzu bata da tsayayyen namiji da suke soyayya.

Da take amfani da yaren kurame da rubutaccen kalamai, kyakkyawar budurwar ta bayyana cewa samari na gudunta saboda ita kurma ce.

Budurwa
Gayu Gudu Na Suke Saboda Ni Kurma Ce, Tsaleliyar Budurwa Ta Koka a Bidiyo Hoto: TikTok/@allthingssimsim
Asali: UGC

Kyakkyawar budurwa mai lalurar kurmanci

Kara karanta wannan

Tsohuwa Mai Shekaru 53 ta Koma Budurwa Shakaf Bayan YI mata Kwalliya a Bidiyo

A karshen dan gajeren bidiyon da tayi, ta kasance dauke da damuwa a fuskarta don nuna halin da take ciki da kuma yadda al’amarin gaba daya ya ishe ta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyonta sun shawarceta da dauki kanta a matsayin mai daraja, suna masu cewa wadanda suka ki yin soyayya da ita sune suka yi babban asara ba ita ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

A daidai lokacin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya tara ‘likes’ fiye da 100,000 sannan mutum fiye 400 ne suka yi martani

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

appleuser832939 ya ce:

“Yakamata koyon yaran kurame ya zama wajibi ga kowa.”

femm ya yi mamaki:

“Ta yaya aka yi kika san sautin da zaki yi amfani da shi.”

Kara karanta wannan

Kungiyar Miyetti Allah tayi watsi da Atiku, tace tana bayan Tinubu/Shettima

Antoine ta ce

“Wannan bai da fa’ida…kina da kyau sosai. Kuma gashi nima kurma ce (amma a kunnena na hagu) don haka ya na san abun da ke tattare da haka.”

Deshawn Green367 ya ce:

“Me zai hana wannan na nufin zaki iya koyawa gaye abubuwa da yawa.”

alwaysjustjohn2 ya ce:

“Zamu koyi yaren kurame yau, hakan ba zai hana komai ba. Jayayyanmu zai zamo baki shiru.

Mirchelle Collins ya ce:

“Ke kyakkyawa ce ‘yar’uwa ki koya masu yadda zasu yi magana da hannu.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng