Turji Ya Shiga Tasku, Sojin Sama Sun Yi Kaca-kaca Da Gidan Mai Kawo Masa Makamai

Turji Ya Shiga Tasku, Sojin Sama Sun Yi Kaca-kaca Da Gidan Mai Kawo Masa Makamai

  • Mallam Ila na kauyen Manawa a jihar Zamfara ya shiga tasku yayin da sojoji suka fatattaki maboyarsa da ke yankin karamar hukumar Shinkafi
  • Rahotanni sun ce, Ila ne babban mai harkallar makamai tare da kasurgumin dan bindiga Bello Turji
  • Sojin Najeriya na ci gaba da samun nasara kan 'yan bindigan da suka addabi jama'a a Arewa maso yammacin Najeriya

Zamfara - A kokari da suke na yakar ta'addanci a fadin kasar, jirgin yakin rundunar sojojin sama ya yi luguden wuta a mabuyar kasurgumin mai safarar makamai, Mallam Ila a kauyen Manawa da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.

Wani jami'in tsaro ya fadama PRNigeria cewa mai safarar makaman shine babban mai kaiwa kasurgumin dan ta'adda Bello Turji muggan makamai a Zamfara.

Yadda sojoji suka ragargaji maboyar 'yan bindiga
Turji Ya Shiga Tasku, Sojin Sama Sun Yi Kaca-kaca Da Gidan Mai Kawo Masa Makamai | Hoto: prnigeria,com
Asali: UGC

Ya ce:

"Jirgin yakin NAF karkashin Operation Hadarin Daji ya kai wani samame kan gidan Mallam Ila a yammacin ranar 18 ga watan Nuwamban 2022.

Kara karanta wannan

Dakarun Soji Sun Murkushe Yan Boko Haram Da Dama Bayan Yi Masu Yayyafin Wuta a Borno

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mallam Ila shine ainahin wanda aka so farmaka saboda kusancinsa da hulda da yake yi da Bello Turji da Dan Bokoyo. Mayakansu sune suka kai hare-hare a karamar hukumar Shinkafi na jihar Zamfara da kuma wasu yankuna na jihohin Kaduna, Neja, Kebbi da Sokoto.
"Bayan samamen da aka kai wajen an lura da fashewar abubuwa da dunkule wuta wanda ke nuni ga akwai abubuwan fashewa boye a wajen. An murkushe wasu yan ta'adda yayin harin."

Wata majiya ta kuma sanar da PRNigeria cewa Mallam Ila ya tsallake rijiya da baya amma ya ji munanan rauni·

Da aka tuntube shi, kakakin NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da samamen sannan ya jaddada cewa ayyukan sojoji na ci gaba da kawar da yan bindiga da yan ta'adda da dama a jihohin.

"NAF da sauran hukumomin tsaro na a kan gabar ganin an zo karshen kokarin da ake na yaki da ta'addanci.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Majalissar Dattijai Omo Ovie-Agege Yace Shine Ya Dakatar da Kudirin Tsige Shugaba Buhari

"Muna kira ga yan Najeriya da su ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro da bayanai kan ayyukan miyagu domin matsalar tsaro da ake fama da shi a yanzu yana bukatar kowa ya shiga ayi da shi."

An ceto mutum 7 daga hannun 'yan bindiga a Kebbi

A wani labarin kuma, an karya lagon 'yan ta'adda a jihar Kebbi yayin da aka yi nasarar kwato wasu jama'ar da suka sace.

An kuma kama wasu mutane da ake zargi da buga kudaden jabu duk dai a jihar ta Kebbi.

'Yan sanda na ci gaba da bincike don gano yadda lamuran suka gudana da kuma yiwuwar daukar mataki na gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng