Ana Tsaka da Shan Soyayya, Budurwa Ta Sharba Wa Saurayinta Wuka Har Lahira
- Jami'an 'yan sanda a jihar Legas sun kama wata mata yar shekara 27, Esther Paul kan zargin halaka saurayinta Sadiq Ɗahiru
- Mai magana da yawun hukumar yan sanda, Benjamin Hundeyin, yace sun samu rahoton lamarin daga mai rikon saurayin
- Mista Hundeyin yace dakaru sun samu wuƙar da aka aikata kisan, yanzun suna kan bincike
Lagos - Hukumar 'yan sanda reshen jihar Legas ta bayyana cewa ta ɗamke wata matashiya, Misis Esther Paul, bisa zargin burma wa Saurayinta, Sadiq Dahiru, wuƙa har yace ga garinku.
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, shi ne ya tabbatar da kama wacce ake zargi mai shekara 27 ga hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN).
Vanguard ta rahoto Hundeyin na cewa an kama budurwar ne ranar Lahadi bayan mai rikon wanda aka kashe, Mista Kazeem Obafunso, ya kai rahoton abinda ya faru Caji Ofis ɗin Ilasan.
Rahoton da hukumar 'yan sandan ta samu a cewar Mista Hundeyin Sadiq Ɗahiru, ya rasa rayuwarsa ne bayan sharɓa masa wuƙa da misalin karfe 1:00 na tsakar dare.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mai magana da yawun yan sandan ya ƙara da cewa bayan karban bayanin nan take aka tura tawagar dakaru daga Caji Ofis ɗin zuwa wurin da lamarin ya faru a kan Layin Oba Amusa, yankin Agungi, Lekki a jihar Legas.
Wane mataki hukumar yan sandan ta ɗauka?
Hundeyin yace jami'ai sun ɗauki gawar Ɗahiru zuwa Asbitin Evecare da ke Lekki, inda Likitin dake aiki a lokacin ya tabbatar da rai ya yi halinsa.
Yace sun kama budurwar kuma sun gano wuƙar da ta yi amfani da ita kana suka kai gawar ɗakin ajiyar gawa na IDH dake Yaba domin gudanar da gwaji da sauran bincike.
Kakakin yace a halin yanzun ana kan bincike kuma za'a maida Kes ɗin sashin binciken aikata manyan laifuka na hukumar yan sandan jihar Legas, The Nation ta rahoto.
A wani labarin kuma Jami'in sashin bincike ya bayyana wa Kotun Kano yadda Ɗan China ya kashe wa Ummita kuɗi sama da miliyan N20m
A zaman Kotu na ranar Jumu'a, Ɓangaren masu gabatar ƙara karkashin kwamishinan shari'a na Kano sun gabatar da shaida na biyar.
Insifekta Injuptil Mbambu, ya faɗa musu yayin bincike cewa ya ba Ummita kudi miliyan N18m ta kama sana'a, ya siya mata gidan miliyan N4m.
Asali: Legit.ng