Dan Sanda Ya Bada Shaida, An Gano Dalilin Da Yasa Dan China Ya Kashe Wa Ummita Miliyoyi

Dan Sanda Ya Bada Shaida, An Gano Dalilin Da Yasa Dan China Ya Kashe Wa Ummita Miliyoyi

  • Jami'in hukumar yan snadan Kano na sashin binciken aikata manyan laifuka ya ba da shaida a gaban babbar Kotu
  • A cewarsa, yayin da suke gudanar da bincike, Ɗan China ya gaya musu yadda ya kashe wa Ummita miliyan sama da N20m
  • Bayan sauraron shaida ta Biyar, Alkalin Kotun ya dage zaman zuwa ranakun 19, 20 da kuma 21 ga watan Disamba, 2022

Kano - A ci gaba da sauraron shari'ar kisan Ummita, ɓangaren gwamnatin jihar Kano karkashin kwamishinan Shari'a, Barista Musa Lawan Abdullahi, sun sake gabatar da shaidu a gaban Alkali.

Jaridar Aminya ta tattaro cewa a zaman ranar Jumu'a da ta gabata, an gabatar da Insifekta Injuptil Mbambu na sashin binciken aikata manyan laifuka ta hukumar yan sandan Kano a matsayin shaida na biyar.

Shari'ar kisan Ummita.
Dan Sanda Ya Bada Shaida, An Gano Dalilin Da Yasa Dan China Ya Kashe Wa Ummita Miliyoyi Hoto: aminiya
Asali: UGC

Jami'in ɗan sandan ya faɗa wa babbar Kotun jiha cewa wanda ake zargi ya musu bayanin yadda ya haɗu da marigayya Ummukulsum watau Ummita har suka fara soyayya.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Fitaccen Malami a Jihar Arewa, Sun Nemi Fansa

A cewar ɗan sandan, wanda ake zargi ɗan asalin kasar China, Mista Cheng, ya faɗa musu cewa Ummita ce ta fara karɓar lambarsa a hannun kawarsa mai suna Hanisa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga nan ne suka fara waya har suka kulla soyayya kuma ta masa alƙawarin zata aure shi a cewar mai ba da shaidar.

Insifekta Ijuptil yace:

"Bayan haka ne (Wanda ake zargi) ya fara kashe mata kuɗi masu nauyi. Yace ya tura mata miliyan N18m domin ta fara sana'a sannan kuma ya saya mata dankareren gida na miliyan N4m."

Legit.ng Hausa ta gano cewa bayan sauraron bayanan jami'in binciken, Alkalin Kotun mai shari'a Sanusi Ado Ma’aji, ya ɗage zaman zuwa watan ƙarshe na wannan shekarar.

Ya zabi ranakun 19, 20 da kuma 21 ga watan Disamban 2022 a matsayin ranar da za'a dawo domin ɗora wa daga inda aka tsaya.

Kara karanta wannan

Kwana 1 Da Yin Wa'azin Mutuwa Bayan Cikarsa Shekaru 40, Allah Ya Yiwa Wani Matashin Gombe Cikawa

Akan Idanunmu ‘dan Chana Ya Damuki Ummita, Ya Burma Mata Wuka a Wuya, Kanwar Ummu

A wani labarin kuma Kanwar Ummita Ta gaya Kotu yadda Ɗan China ya daɓa wa Ummita Wuka a kan idanunsu a cikin ɗakinta

Asiya Sani Buhari, kanwa ga marigayya Ummukulthum bayan buɗe masa Ƙofa, Mista Cheng ya shigo ta kama Ummita, ya shiga ɗaki ya kulle kofa.

Ta ƙara da cewa nan da na suka leka ta taga suka hangi ya zare wuƙa, Ummita na bashi hakuri amma ya shatɓa mata a wuya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262