Ayu Barawo Ne, Ya Fara Gina Jami'a a Jihar Benue: Nyesom Wike
- Nyesom Wike ya sake wani sabon zargi da yake yiwa shugaban jam'iyyarsa ta PDP, Iyorchia Ayu
- Wannan kusan shine karo na uku da Wike ya tuhumi Ayu da wawurar kudin jam'iyya don amfanin kansa
- Shi ko Ayu har ila yau bai mayar da martani ba, yace masu zaginsa kananan yara ne lokacin da aka kafa PDP
Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya sake caccakan Shugaban uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Dr. Iyorchia Ayu, ranar Asabar, 19 ga watan Nuwamba.
Wike ya jaddada cewa jagoran na PDP babban barawo ne kuma ya fara gina sabuwar jami'a mai zaman kanta a jihar Benue cikin shekara daya da hawa mulki.
Wike ya kalubalanci Ayu ya kai shi kara kotu idan karya yake masa, rahoton TheNation.
Wike ya bayyana hakan ne wajen taron kaddamar da yakin neman zabe PDP a jihar Rivers da akayi a filin kwallon Adokiye Amiesimaka, Port-Harcourt, rahoton ChannelsTV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yace:
"Ayu mai rashawa ne. An zalunci al'ummar Rivers, ta yaya ake yaki da rashawa kan ikirain kana yaki da rashawa? Na sace ya karbi N1bn. Na fada maka ka karbi kudin da muka sanu lokacin zaben fidda gwani, Ayu kai ni kotu."
"Ba zaka iya yakar jihar Rivers ka sha ba."
Wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamna Samuel Ortom (Benue), Seyi Makinde (Oyo), Okezie Ikpeazu (Abia), da Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu).
Hakazalika akwai mataimakin shugaban PDP, Taofeek Arapaja da tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose.
Wike Ya Caccaki Atiku Kan Sukan Shugaba Buhari
A wani labarin kuwa, Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya caccaki dan takarar kujerar shugaban kasan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, kan suka da ya yiwa shugaba Muhammadu Buhari.
Atiku a ranar Laraba ya soki shugaba Buhari kan baiwa yan Arewacin Najeriya 17 mukaman shugabannin tsaro,
Wike ya ce Atiku munafuki ne saboda meyasa bai fadi hakan tun shekarun baya ba sai yanzu da zabe ya kusanto.
A jawabin da yayi ranar Alhamis, 17 ga Nuwamba Wike yace idan Atiku da gaske yake, ya fara tabbatar da adalci tsakanin 'yayan jam'iyyarsa ta PDP tukun kan ya zagi shugaba Muhammadu Buhari.
Asali: Legit.ng