Zafi Biyu: An Harbi Jami'in Dan Sanda A Azzakari, Kaninsa Ya Dirkawa Matarsa Ciki

Zafi Biyu: An Harbi Jami'in Dan Sanda A Azzakari, Kaninsa Ya Dirkawa Matarsa Ciki

  • Dan Sanda ya dawo gida daga wajen horo ya tarar kaninsa ya tayashi dirkawa matarsa juna biyu
  • Hafsan ya ce musamman ya kama daki a cikin gida daya da kaninsa saboda ya tayashi kula
  • Jami'in dan sanda ya bada labarin abinda ya faru tsakanin Amaryarsa da kaninsa na jini

Lafia, Nasarawa - Wani jami'in dan sanda, Japhet Aba, a jihar Nasarawa ya gamu da abin mamaki yayinda ya dawo gida bayan watanni tara da ya tafi horo jihar Bauchi.

Japhet dan asalin karamar hukumar Doma ya tafi horon ne watanni uku bayan aurensa da Amarya, Angela Onuh.

Dawowarsa ke da wuya ya tarar kaninsa, Samuel Aba, ya dirkawa matarsa ciki.

Japhet a hirarsa da TheNation ya laburta cewa ya kama daki a gidan da Samuel yake don ya taya shi kula da matarsa kafin ya dawo.

Kara karanta wannan

An Kona Gidan Jigon PDP Awa 24 Bayan Gwamna Ya Masa Kyautar Sabuwar Mota A Babban Jihar Arewa

A cewarsa, Samuel malamin makarantar firamare ne kuma matarsa tace shine ya tilasta mata kwanciya da shi har ta samu ciki.

A jawabin da tayi masa, tace ta ni niyyar zubar da cikin amma taji tsoro saboda mahaifiyarta ta gargadeta kan ta mutu cewa idan ta zubar da ciki za ta mutu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yace:

"Na auri matata a Satumba 2021. Kafin aure mun yi yarjejeniyar cewa ba zamu sadu da juna ba har sai mun yi aure, kuma hakan mukayi."
"Gabanin tafiya na horon aikin dan sanda, mun tattauna kan rayuwarmu. Kasancewana 'da namiji daya tilo wajen mahaifiyata, ta kosa in haifa mata jika, amma ni da matata muka yanke shawarar jinkiri tunda zan tafi sansanin horo."
"Kullun muna waya da ita. Abin mamaki shine da na dawo na tarar da cikin da ban san da shi ba. Sai ta fada min cikin kani na ne wanda na baiwa amana."

Kara karanta wannan

Yadda Matar Aure Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Ya Mutu Yayin Da Ya Kusance Ta Don Ƙoƙarin Neman Hakkinsa Na Aure Daga Gare Ta

"Ashe Shaidan zai yi amfani da dan'uwana wajen lalata aure na."

Dan sanda
Jami'in Dan Sanda Ya Dawo Gida Bayan Wata 9, Ya Tarar Kaninsa Ya Dirkawa Matarsa Ciki
Asali: Facebook

Kanin da yayi aika-aikan, Samuel Ya Mutu

Japhet ya bayyana cewa ya kalubalanci kaninsa Samuel kan yadda hakan ya auku, yace:

"Samuel ya fada min cewa Amaryata ta fada masa ni rago ne a cikin daki kuma ba na gamsar da ita duk da cewa tana so na. Tana bukatan Namiji mai karfi da zai gamsar da ita."
"Ya ce yana tsoron kada ta fita wajen neman maza shi yasa yace bari ya taimaka."
"Samuel din ya mutu yanzu. Ya mutu sakamakon harin makiyaya yayinda ya tafi gona a kauye. Ina rokon Allah ya yafe masa kura-kuransa."

Shawarar da Japhet ya yanke

Dan sandan ya bayyana cewa kawai ya yanke shawarar komawa bakin aiki saboda ya 'dan wuce daga radadin abinda ya faru.

Yace ya bar gidan kuma ya rabu da matar ta yanke shawara da kanta.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shahararren Mawakin Bishara Na Najeriya Ya Yanke Jiki, Ya Mutu A Gidansa A Legas

Yace:

"Da wuri na koma bakin aiki don barin matata ta yanke shawaran da ya fisheta. Amma a raina na yanke shawarar cewa babu ni, babu ita har abada. Mun daina waya da juna."

Shima Japhet ya gamu da Ibtila'i

Shima da Angon ya gamu da jarabawa inda aka harbesa a azzakari a bakin aiki yayinda suke musanya wuta da wasu yan fashi.

Yanzu haka yana kwance a asibiti dake Lafia, ita kuma matarsa Angela har ta haifi 'da namiji.

Yace har yanzu bai samu daman gani sabon jariin ba.

Yace:

"Na yanke shawarar fadawa duniya ne saboda halin da nike ciki a asibiti. Da yiwuwan ba zan tashi ba kuma ina son duniya ta samu labari."

Asali: Legit.ng

Online view pixel