Shugaba Buhari Ya Amince Da Karin Albashi Ga Wasu Ma'aikata
- Ma'aikatan kotunan Najeriya suyi shewa, shugaba Buhari ya amince a yi musu karin albashi
- Ministan Shari'a yace an umurci ma'aikatar biyan albashi (RMAFC) ta gaggauta aiwatar da wannan tsari
- Bangaren Shari'a na daya daga cikin sassan gwamnati uku masu zaman kansu amma duk da haka suna kukan karancin albashi
Port Harcourt - Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da karin albashi ga ma'aikatan shari'a a Najeriya.
Shugaban kasan ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a birnin Fatakwal, jihar Rivers, yayin bikin kaddamar da sabon makarantar lauyoyi da gwamna Nyesom Wike ya gina.
Buhari, ya samu wakilcin Antoni Janar kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami SAN, rahoton ChannelsTV.
Malami ya bayyana cewa Shugaban kasan ya amince da karin albashin ne saboda baiwa ma'aikatan Shari'a karfin zaman kansu da kuma wanzar da gaskiya.
A cewarsa:
"Shugaban kasa ya amince da karin albashi da ma'aikatan shari'a kuma tuni an umurci shugaban hukumar biyan albashi da ofishin Antoni Janar na tarayya da ministan shari'a su fara tsarin aiwatar da karin."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi alkawarin cewa gwamnatin Buhari za ta cigaba da kokarin kawo sauye-sauye masu amfani bangaren shari'a.
A bidiyon da ChannelsTV ta fitar, Ya jinjinawa Gwamna Wike bisa kammala wannan makaranta cikin shekara guda kacal.
Yace wannan shine dalilin da yasa Buhari yayi watsi da banbancin siyasa ya baiwa Nyesom Wike lamba yabo a Oktoba.
Wannan gini shine makarantar Lauyoyi na bakwai a Najeriya.
Wike Ya Caccaki Atiku Kan Sukan Shugaba Buhari
A wani labarin kuwa, Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya caccaki dan takarar kujerar shugaban kasan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, kan suka da ya yiwa shugaba Muhammadu Buhari.
Atiku a ranar Laraba ya soki shugaba Buhari kan baiwa yan Arewacin Najeriya 17 mukaman shugabannin tsaro,
Wike ya ce Atiku munafuki ne saboda meyasa bai fadi hakan tun shekarun baya ba sai yanzu da zabe ya kusanto.
A jawabin da yayi ranar Alhamis, 17 ga Nuwamba Wike yace idan Atiku da gaske yake, ya fara tabbatar da adalci tsakanin 'yayan jam'iyyarsa ta PDP tukun kan ya zagi shugaba Muhammadu Buhari.
Asali: Legit.ng