Karban Bashin Fa Ya Isa Haka, Diraktar Ofishin Tattalin Basussuka DMO Ya Gargadi Gwamnatin Tarayya
- Kawo yanzu ana bin Najeriya bashin N42.8 trillion; N26.2 trillion na gida, N16.6 trillion na waje
- Yanzu Najeriya na karban bashin kudade don biyan tsaffin basussukan da aka karba a shekarun baya
- Gwamnatin tarayya ta ce karban basussukan sun zama wajibi ne saboda kudin shiga sun daina isa
Abuja - Ofishin Manejin basussukan Najeriya (DMO) ya bayyana cewa akwai bukatar gaggawa na gwamnatin tarayya ta rage karban basussuka don a iya biyan na kasa.
Dirakta Janar na ma'aikatar DMO, Patience Oniha, ta bayyana hakan ranar Alhamis a wani waksho da aka shiryawa yan majalisa, rahoton TheCable.
Ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta nemo hanyar rage kashe kudi, samar da isassun kudin shiga sannan kuma a tabbatar bashin da za'a karba ayyuka za'a yi dasu wadanda ribar za'a samu da su zasu iya biyan bashin.
Tace yanzu basussukan gida da na waje sun yiwa Najeriya katutu kuma kudin rawa na kara yawa, riwayar BusinessDay.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarta,
"Saboda haka ya kamata a rage karban bashi kuma a mayar da hankali kan samar da kudin shiga daga bangaren man fetur da sauransu."
"Basussukan da ake bin Najeriya sun yi yawa a tsawon shekarun nan. Haka yasa kudin ruwan dake hawa na kara yawa."
"Dogaro kan arzikin man fetur ke haddasa rashin samun isassun kudin shiga."
A cewarta, kawo watan Yuni 2022 dai ana bin Najeriya bashin N42.8 trillion (N26.2 trillion na gida, N16.6 trillion na waje).
Game da bashin da kasar Sin ke binmu kuwa, Oniha yace $3.6 billion ne kacal.
A cewarta:
"Saukin abun shine bashin kasar Sin na aiki ne. Bamu dogara da shi ba. Bai da yawa amma saboda aiki ake da shi yana da kyau."
Najeriya yanzu bashi muke karban don biyan wani bashin da akaci a baya, Sanusi
A wnai labarin kuwa, tsohon gwamnan bankin CBN kuma Sarkin Kano na 14, Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana cewa yanzu fa Najeriya bashi ake karba don biyan wani bashin.
Sanusi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na tarawa jikoki da tattaba kunne bashi.
Tsohon Sarkin yace Najeriya babu wani cigaba da take da alaman samu nan gaba.
Asali: Legit.ng