Idan Muka Yiwa Yan Najeriya Karya Wuta Zamu Shiga, Oshiomole Ga Yan Siyasa
- Tsohon shugaban APC, Adams Oshiomole, ya shawarci abokansa yan siyasa su daina sharara karya
- Oshiomole ya ce yan siyasa su daina yiwa al'umma alkawuran da suka san ba zasu iya cikawa ba
- Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya gayyaci Oshiomole kaddamar da wani titin sama da aka kammala ginawa
Rivers - Tsohon Gwamnan jihar Edo kuma tsohon Shugaban uwar jam'iyyar jam'iyyar All Progressives Congress APC, Adams Oshiomole, ya gargadi yan siyasa kan karya.
Oshiomole wanda ke neman takarar kujerar Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa karkashin APC a zaben 2023 yace duk dan siyasar da ke yiwa al'ummarsa karya cikin wuta zai kare.
Ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin kaddamar da titin saman Rumuepirikom dake karamar hukumar Obio-Akpor a jihar Rivers, rahoton Peoples Gazette.
Yace:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A addini da nake yi, karya haramun aka ce, idan siyasa ta zama karya, toh dukkanmu wuta zamu kare. Ban son zuwa wuta. Ina fatan idan na bar duniyar nan in tafi waje mai kyau."
"Idan yan siyasa sukayi alkawari kuma suka gaza cikawa sai suce haka siyasa take."
Oshiomole ya tona asirin wasu gwamnoni, ya ce suna ba tsageru bindigogi AK-47 a lokacin zabe
A wani labarin kuwa, Adams Oshiomole yayi bayanin yadda wasu gwamnoni ke taka rawa wajen dagula lamuran kasar nan musamman lokutan zaben.
Oshiomole ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da kungiyar YIAGA Afrika ta shirya tare da hadin gwiwar majalisar dinkin duniya da gidan talabijin na Channels.
A bayaninsa, ya kamata jam'iyyun siyasa su rika wayar da kan mabiyansu cewa zabe 'yanci ne kuma ba yaki bane.
Jawabinsa:
"Ya kamata mu ke fadawa shugabanninmu cewa, dole su yi da'awar yin zabe ba tare da tashin hankali ba. Ina sake nanata cewa, dukkanmu aiki ne a kanmu. Najeriya ta fi gaban dukkan jam'iyyun siyasa."
"A lokacin da nake gwamna (a jihar Edo) na fadi haka, ku tambayi (tsohon) shugaban kasa Goodluck Jonathan, na tada batu a wata ganawa a Villa cewa, wasu gwamnoni a wasu lokutan na taimakawa wajen tada hankali a lokacin zabe saboda AK-47 ba abu ne mai araha ba kamar kosai.
Asali: Legit.ng