An Cigaba da Sauraron Shari'ar Dan China, Makoci Ya Bada Shaida a Kotu

An Cigaba da Sauraron Shari'ar Dan China, Makoci Ya Bada Shaida a Kotu

  • A ranar Alhamis ɗin nan ne aka ci gaba da sauraron shari'ar wanda ake zargi da kashe Ummita a Kano
  • Bangaren masu shigar da ƙara karkashin jagorancin kwamishinan Shari'a na Kano sun gabatar da shaida ta uku
  • Makocin gidansu marigayya Ummita, Mustapha Abubakar, ya labarta yadda lamarin ya faru tun farko

Kano - A ci gaba da zaman Kotu kan shari'ar kisan Ummita wanda ake zargin saurayinta ɗan asalin ƙasar China mazaunin Kano da aikata wa, an saurari shaida ta uku ranar Alhamis.

Jaridar Aminiya ta tattaro cewa ɓangaren masu shigar da ƙara karkashin Kwamishinan shari'a na jihar Kano, Barista Musa Lawan Abdullahi, sun gabatar da makocin gidansu Ummita.

Ummita.
An Cigaba da Sauraron Shari'ar Dan China, Makoci Ya Bada Shaida a Kotu Hoto: aminiya
Asali: UGC

Mutumin mai suna, Mustapba Abubakar, makocin gidan, ya faɗa wa Kotun cewa shi ne ya ɗaga wanda ake zargi daga kan marigayya Ummita bayan ya daɓa mata wuka.

Kara karanta wannan

2023: Na Gano Matsalar Najeriya, Abu Ɗaya Ne Tal, Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Magantu

A bayanansa, yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ranar da aka yi kisan, ana ruwa ina kokarin kiran waya amma Sabis ya ƙi bani haɗin kai sai na fito waje anan ne na ci karo da Ɗan China yana ta buga ƙofar gidansu Ummita da ƙarfi."
"Ganin haka ya sa na karisa nace masa ya jira zasu zo su buɗe, sai ya koma cikin motarsa ya ɗakko waya yana latsa wa, ni kuma na kama gabana na bar layin Anguwar."

Yadda na kaiwa Ummita ɗauki har ɗaki - Makoci

Malam Mustapha ya ƙara da cewa yana dawo wa layin Anguwar sai ya taras mahaifiyar Ummita na ta kururuwar neman taimako, tana cewa za'a kashe mata ɗiya.

"Babu wata wata na afka cikin gidan na ci karo da ƙannenta suna ta rusa kuka, na je shiga ɗakin a kulle, na kutsa da taga, ina shiga na ga Geng a kan gadon yarinyar kaman suna kokawa, ina jawo shi naga wuƙa a hannunsa da jini."

Kara karanta wannan

Mutanen Jihata Zasu Angiza Wa Tinubu Tulin Kuri'unsu, Atiku Bai da Rabo, Gwamna Ya Magantu

"Ita kuma Ummita jini ne ta ko ina a jikinta tana faman kakari. Na yi kokarin ɗaga ta amma ta yi nauyi, sai na kira wani mai shayin Anguwarmu na nemi ya kira Likita ko ya zo da wasu a taimaka mana."
"Yana zuwa muka ɗauketa a Motar wanda ake zargi aka tafi da ita Asibiti amma ni banje ba saboda jini ya ɓatamun riga na shiga gida na canza."

A wani labarin tun zaman jiya Laraba kanwar marigayya Ummita da kuma mahaifiyarta sun ba da shaida kan Mista Geng a Kotu

Aisha Sani Buhari ya faɗa wa Kotu ana buɗe masa ƙofa, ya shigo da karfi ya cafki Ummita kana ya yi cikin ɗakinta da ita kuma ya kulle ƙofa.

Ƙanwar ta shaida wa Alkali cewa nan take suka leka suga meke shirin faruwa, kawai suka hangi ya zare wuƙa, Ummita na kokarin ba shi hakuri amma ya daɓa mata a wuya.

Kara karanta wannan

Matata Ta Zuba Mun Guba Kuma Bata Ganin Girma Na, Miji Ya Nemi Kotu Ta Raba Aurensa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262