IGP Ya Bayyana Gwamnoni Na Ɗaukan Nauyin Kaiwa Abokan Hamayarsu Hari A Jihohinsu

IGP Ya Bayyana Gwamnoni Na Ɗaukan Nauyin Kaiwa Abokan Hamayarsu Hari A Jihohinsu

  • Sufeta Janar na yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya yi zargi wasu gwamnoni na daukan nauyin hare-hare da aka kaiwa yayin kamfen a jihohinsu
  • A cewar Baba, an samu hare-haren guda 52 yayin kamfen din siyasa tun fara yakin neman zaben shugaban kasa na 2023
  • Shugaban yan sandan ya ce jami'an tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba wurin daukan mataki kan duk wani da aka kama yana tada hankula

FCT, Abuja - Shugaban rundunar yan sandan Najeriya. Usman Alkali Baba ya yi zargin wasu gwamnoni ke daukan nauyin yan daba da ke kai hare-hare yayin kamfen din abokan hamayyarsu.

Shugaban yan sandan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis 17 ga watan Nuwamba, yayin da ya ke magana da jam'iyyun siyasa da hukumar zabe mai zaman kanta INEC da masu ruwa da tsaki a zaben 2023, Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rigimar PDP: Tsagin Gwamna Wike G5 Sun Gindaya Sharudda a Sabon Shirin Sulhu da Su Atiku

Alkali Usman
IGP Ya Bayyana Gwamnoni Na Ɗaukan Nauyin Kaiwa Abokan Hamayarsu Hari A Jihohinsu, Hoto: Rundunar Yan Sandan Najeriya.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abin da ke faruwa kan APC, PDP, Yan Sanda, Usman Alkali-Baba, Zaben 2023, INEC

Amma, Alkali-Baba bai ambaci sunayen gwamnonin ba yayin da ya ke bayyana cewa an kawo yanzu an samu hare-haren siyasa 52 tun fara yakin neman zaben shugaban kasa na 2023.

Ya ce yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba wurin magance matsalar da ke tasowa.

Shugaban yan sandan ya kuma gargadi yan siyasa kan muggan abubuwa da ka iya kawo matsala a zaben na 2023.

IGP ya bayyana hatsarin da ke tattare da rikici a zaben shugaban kasa na 2023

IGP din ya kara da cewa a baya, tashin hankula yayin zabe ya kasance barazana ga cigaban demokradiyya.

Wani sashi na sanarwarsa ta ce:

"Wannan taron ya zama dole biyo bayan abin da ke neman zama ruwan dare a kasar, idan ba a magance shi cikin gaggawa ba zai iya rikidewa ya zama barazana ga tsaron kasa da ma zaben."

Kara karanta wannan

Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 2023: Jerin Buƙatun Da Shugabannin CAN Suka Gabatarwa Tinubu A Abuja

2023: Yan Daba Sun Kai Wa Jirgin Yakin Neman Zaben Dan Takarar Gwamna Na PDP Hari

Wasu yan daba sun kai wa jirgin yaƙin neman zaben Olajide Adediran, ɗan takarar gwamnan jihar Legas karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zaben 2023 hari.

A wata sanarwa da shugaban PDP reshen Legas, Hakeem Amode, ya fitar, ya ce an farmaki Adediran wanda aka fi sani da Jandor a yankin Ikoga junction, karamar hukumar Badagary ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164