Soji Sun Sheke Kachalla Gudau da Rigimamme, Manyan Kwamandojin ‘Yan Bindiga
- Dakarun sojin Najeriya sun halaka gawurtaccen kwamandan ‘yan bindiga kuma gogaggen dillalan kwayoyi da satar shanu, Kachalla Gudau a jihar Kaduna
- An gano cewa, a cikin wata 6 kacal, Gudau da mukarrabansa sun sace Shanu 6,532 a Kajuru ta jihar Kaduna inda ya siyar dasu tare da zama miloniyan barawo
- Gudau kafin haduwa da ajalinsa, yana amfani da kudin shanun wurin dillancin miyagun kwayoyi tare da safarar makamai yana siyarwa
Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna a ranar Laraba tace jami’an tsaro a Najeriya sun halaka hatsabibin kwamandan ’yan ta’adda, Kachalla Gadau, Samuel Aruwan ya bayyana shafinsa na Twitter.
“Gadau, hatsabibin ‘dan bindiga wanda ke umartar ‘yan bindiga masu tarin yawa wurin garkuwa da mutane da kashe-kashe a kananan hukumomin Chikun, Kachia da Kajuru yana daga cikin ‘yan bindigan da dakarun sojin Najeriya suka halaka a ranar Lahadi a Kankomi dake jihar Kaduna.”
- Cewar Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna.
“Amfani da bayanan sirri ya tabbatar da cewa Gudau yana daga cikin wadanda harsashin zakakuran dakarun sojin Najeriya ya halaka a yayin dakile farmakin da gagararren ‘dan bindigan da kansa ya jagoranta wanda hakan ya kawo karshen shaidancinsa da zaluncinsa.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- Aruwan ya kara da cewa a shafinsa na Twitter.
Yace tuni ‘yan kungiyarsa suka dauke gawar ‘dan ta’addan daga dajin Kankomi inda ya dinga zubar da jini har ya mutu.
Aruwan yace bayanai gamsassu sun rahoto cewa bayan sun dauka gawarsa, ‘yan bindigan dake karkashinsa masu tarin yawa sun birne shi wuraren dajin Kaku dake Kaso a karamar hukumar Chikun.
Wani ‘dan ta’adda da ake kira da Rigimamme ya sheka lahira a wannan arangamar. Yana daya daga cikin manyan sojojin Gudau, Aruwan ya kara da cewa.
Gudau ya kasance na kan gaba a wurin shirya garkuwa da ‘yan makaranta da bakin haure a kananan hukumomin Kajuru, Chikun da Kachia.
Yace ‘dan ta’addan ya shahara wurin halaka wadanda ya sace ko kuma suka gwada masa taurin kai yayin da yaje sacesu.
Satar shanu da harkar miyagun kwayoyi
Aruwan ya sanar da cewa, marigayin ‘dan ta’addan mashahuri ne a wurin satar shanun jama’a kuma dillalin miyagun kwayoyi ne.
“Bugu da kari kan miyagun ayyukansa, Gudau ya kasance mai tsara hari kan makiyaya, satar dabbobi, wanda hakan yasa ya mallaki shanun sata masu yawa.
“Yana yawan siyar dasu kan miliyoyin kudi. Daga nan yake safarar miyagun kwayoyi da makamai masu hatsari.
“Yayi shuhura wurin satar shanun a watanni shida na farkon 2022 inda a karamar hukumar Kajuru kadai Gudau da mukarrabansa suka sace shanu 1,600 da wasu 4,932 a watanni uku uku.”
- Aruwan yace.
Asali: Legit.ng