Janar din Soja Ya Sheka Lahira Bayan Direban da Yayi Tatil Ya Bankesa a Titi

Janar din Soja Ya Sheka Lahira Bayan Direban da Yayi Tatil Ya Bankesa a Titi

  • Birgediya Janar Audu James, na rundunar sojin kasan Najeriya ya kwanta dama bayan banke shi da direba yayi a kan titin Legas
  • Kamar yadda takardar da Kayode Olagunju, jami’in walwala na SEC 40 ya bayyana a ranar Laraba, ya rasu sakamakon raunikan da ya samu
  • Olagunju ya bayyana alhininsa kan wannan babban rashin da suka yi yayin da yake mika ta’aziyyarsa ga dukkan iyalansa

Legas - Audu James, Birgediya janar a rundunar sojin Najeriya ya rasu bayan wani mai abun hawa a Legas ya banke shi, jaridar The Cable ta rahoto.

Birgediya Janar
Janar din Soja Ya Sheka Lahira Bayan Direban da Yayi Tatil Ya Bankesa a Titi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

James wanda shi ke kula da National Institute for Policy and Strategic Studies dake Kuru a jihar Plateau, ya rasa ransa a ranar Laraba baya ya samu miyagun raunika sakamakon bige shi da direba yayi a ranar Talata a Legas.

Kara karanta wannan

Yadda ‘Dan Majalisar Legas Ya Rasu Wajen Taron Kamfen Bola Tinubu a Garin Jos

Rundunar Soji ta fitar da sanarwa

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, Kayode Olagunji, jami’in walwala na Senior Executive Course 40, a wata takarda da aka fitar a ranar Laraba, yace mutuwar James abun takaici ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Labari mara dadi. Mun rasa mutum mai amfani. mara gajiyawa, mai saukin kai, monitor janar na SEC 40 na National Institute for Policy and Strategic Studies, Kuru, Birgediya Janar Audu Ogbole James.”

- Takardar tace.

“Ya rasu ne sakamakon raunikan da ya samu a bige shi da aka yi a titi jiya, 15 ga Nuwamban 2022 da yammaci a Legas. Muna masa fatan rahama ballantana SEC 40.
“Ubangiji ya ba dukkanmu hakurin jure wannan rashin da ba za mu iya mayar da madadinsa ba.”

- Ya kara da cewa.

Yan ta’adda sun shiga tasku

Kara karanta wannan

Tashin Hankali, Bayan Yayi Tatil da Giya, Kofur Ya Buge Babban Janar Da Mota Har Lahira

A daya bangaren, jami’an tsaro suna cigaba da matsawa ‘yan ta’adda lamba.

A ranar Lahadi, dakarun soji sun dakile farmakin ‘yan bindiga a sansanin soji dake Chikun dake jihar Kaduna.

Ba su tsaya nan ba, sun halaka 2 daga cikin ‘yan bindigan tare da dira sansanoninsu inda suka ragargaji wasu.

Sai dai cike da takaic sun tsinci gawar mutum 3 a kan hanya wanda ake kyautata zaton ‘yan bindigan da suka tsere ne suka halaka su.

A wani cigaba a ranar Asabar, jami’an tsaro sun halaka ‘yan bindiga biyar da Isuofia dake karamar hukumar Aguata dake jihar Anambra.

Aguata ce karamar hukumar Chukwuma Soludo, gwamnan jihar Anambra.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng