Asiri Ya Tonu: An Kama Wata Mota Makare da Bindigu a Kofar Shiga Babbar Kotun Jiha
- Jami'an tsaro sun kama wata mota maƙare da bindigogi da wasu mutane a kofar shiga harabar babbar Kotun jihar Osun
- Mai magana da yawun yan sandan jihar, Yemisi Opalola, tace bayan zuwa Hedkwata an gano su waye a cikin motar
- A cewarta mafarauta masu taimaka wa yan sanda a aikin tsaro ne a motar ɗauke da makamansu, saɓani kawai aka samu
Osun - Wata Mota ɗauke da mutane da kuma Bindigu ta shiga hannu a ƙofar shiga harabar babbar Kotun jihar Osun ranar Laraba.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru yayin da aka dawo zaman ci gaba da sauraron ƙorafe-korafe daga zaɓen gwamnan jihar da aka yi ranar 16 ga watan Yuli.
Gabanin fara zaman, an girke Jami'an tsaro a kofar shiga harabar Kotun suna gudanar da bincike kan duk wata mota dake son shiga wurin.
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa yace Motar da ke ɗauke da bindigogin ta shiga hannu ne yayin da ta yi kokarin shiga harabar Kotun.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ba tare ba ɓata lokaci ba bayan kama Motar, jami'an yan sanda suka tasa ta tare da mutanen dake ciki zuwa sashin binciken aikata manyan laifuka a Hedkwatar 'yan sandan jihar, Osogbo.
Su waye aka gano a cikin motar?
Da aka tuntuɓeta, mai magana da yawun hukumar yan sanda reshen jihar Osun, Yemisi Opalola, ta tabbatar da lamarin. Ta yi bayanin cewa waɗanda ke cikin Motar mafarauta ne dake taimaka wa yan sanda.
A kalamansa ta ce:
"Mafarauta ne da ke aikin ba da tsaro, ba bu wanda suka kai wa hari, sun aiki tare da dakarun 'yan sanda domin tabbatar da tsaro. Babu wani abun damuwa."
"Wani wuri daban suka nufa daga bisani kuma aka umarce su da su koma wanna wurin."
A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Harbe Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Har Lahira a Nasarawa
Bayanai sun nuna cewa matar mai suna Success na kan hanyar zuwa kasuwa ba zato maharan suka buɗe wa motar da take ciki wuta da misalin karfe 9:00 na safe.
An ce kafin rasuwarta, matar ta kasance fitacciyar yar kasuwa a yankin kuma ana zargin maharan basu so kasheta ba amma harsashi ya sameta.
Asali: Legit.ng