Mata, Miji Da ’Ya’yansu Hudu Sun Mutu Bayan Cin Abincin Dare a Jihar Anambra
- An shiga jimami yayin da aka gano wasu ahali sun mutu gaba dayansu a rana daya bayan da suka ci abincin dare
- Majiyar kusa da dangin ta bayyana cewa, akwai alamu masu karfi da ke nuna an sanya guba ne a abincin ahalin
- Ana yawan samun iftila'in mutuwa ahali guda a lamuran da suka shafi abinci, musamman a Najeriya
Jihar Anambra - Wani mutum mai suna Mr Augustine Nwokedi, matarsa da 'ya'yansa hudu sun rasu jim kadan bayan cin abincin dare a Ozubulu, jihar Anambra.
An tattaro cewa, wannan lamari ya faru ne a ranar 4 ga watan Oktoba, an ce makwabta ne suka gano gawarwakin mamatan a gidan bayan faruwar lamarin da dan lokaci.
Wata majiya ta shaida cewa, lamarin ya faru ne bayan da ahalin suka ci abincin dare kana suka shiga don su kwanta, amma aka gano sun gaba dayansu da safe.
Hasashen dalilin mutuwa ahalin gaba dayansa
Majiyar ta ce, ana zargi ahalin sun mutu ta dalilin cin abincin da aka saka masa guba ne, amma dai ba a tabbatar da hakan ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
'Ya'yan mamatan, maza ne guda uku da mace daya, wadanda basu wuce shekaru uku zuwa 12 ba, inji rahoton Punch.
An ce mai gidan ya kai shekaru 41, matarsa kuwa mai suna Josephine Nwokedi ta kai shekaru 39, Daily Post ta tattaro.
Ya zuwa yanzu dai, an sanya ranar 29 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a yi jana'izarsu wadannan mamata gaba dayansu.
Ba sabon abu bane a Najeriya, musamman ahali guda saboda cin abincin da ke gurbace da guba ko dai wani abin daban.
Yadda 'yan sanda suka bankado gawarwakin mutum biyu da suka mutu a daki, an samu firgici
A wani labarin kuma, an tsinci gawar wani mutum da wata mata a wani gida a jihar Bauchi, lamarin da ya tada hankalin mazauna yankin.
Rahoton da 'yan sanda suka fitar ya bayyana cewa, an bankado gawarwakin guda biyu ne kwanaki da dama bayan sun mutu yayin da suke kwance a daki.
Ya zuwa yanzu dai an tattara su zuwa asibiti domin tabbatar da dalilin mutuwarsu da kuma shirya jana'iza a nan gaba.
Asali: Legit.ng