Tinubu Ba Subut-da-baka yai ba, Allah Ne Ya Matsi Bakinsa: PDP

Tinubu Ba Subut-da-baka yai ba, Allah Ne Ya Matsi Bakinsa: PDP

  • Babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta shiga yiwa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Isgili bisa katobarar da yayi a Jos
  • PDP tace mutane fa kada suyi mamakin yanda Tinubu ke baranbarama, Allah ne ya matsi bakinsa yayi mata addu’a
  • Dan takaran shugaban kasan APC ranar Talata a Jos ya kuskure yayindayake kokarin yiwa jam’iyyarsa addu’a

Abuja - Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa kuskuren da Bola Tinubu, dan takaran shugaban kasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yayi a wajen taron kaddamar da kamfensa ba subut-da-baka bane.

PDP tace kawai Allah ne ya matsi bakinsa ya yiwa jam’iyyar adawa addu’a kuma wannan na tabbatar da rashin cancantarsa.

Kakakin jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, a jawabin da ya fitar da yammacin Talata yace addu’ar Tinubu ta tabbatar da cewa jam’iyyar PDP Allah ke son baiwa mulki.

Kara karanta wannan

Nayi babban kuskure: Bidiyo Ya Nuna Osinbajo Ya Nemi Afuwar Mai gidansa, Tinubu

Tinubu
Tinubu Ba Subut-da-baka yai ba, Allah Ne Ya Matsi Bakinsa: PD Hoto: Buhari Sallau
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

Ba subut-da-baka yayi ba, Allah ne ya matsi bakinsa kuma hakan ya faru ne saboda PDP ce zata iya seta rana goben Najeriya.”
“Hazakalika a jawabinsa, dan takaran APC ya tabbatar da cewa yan Najeriya na cikin halin kakanikaye saboda gwamnatin APC ta gaza amma shi zai gyara.”
“Ya bayyana karara cewa Tinubu na wadannan kura-kuren ne saboda bayyanar labarin yadda yayi safarar kwaya a Amurka, wanda hakan ya tada masa da hankali matuka kuma ya rikice saboda kowa ya san bai cancanci zama shugaban kasar Najeriya ba.”
“La’alla shine dalilin da yasa yake ta kame-kame wajen taron kaddamar da kamfensa.”

Debo ya kara da cewa Tinubu fa gaba daya ya kidime da yadda dan takaran PDP, Atiku Abubakar ya samu karbuwa.

“Saboda haka, muna bashi shawara kawai ya baiwa yan Najeriya hakuri kuma ya janye daga takarar,” Debo ya kara.

Kara karanta wannan

Wani Gwamna Ya Jingine Tinubu, Atiku da Peter Obi, Ya Faɗi Wanda Yake Goyon Bayan Ya Gaji Buhari a 2023

Kalli bidiyon:

Dan majalisar dokoki ya mutu a filin kamfe

Wani dan majalisar dokokin jihar Legas, Honorabul Sobur Olayiwola, ya yanki jiki ya faɗi ana tsaka da gangamin Bola Tinubu a Jos.

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Mushin II a majalisar dokokin jihar Legas, Honorabul Sobur Olayiwola, na daga cikin waɗanda suka halarci buɗe kamfen APC a Jos.

An tattaro cewa ɗan siyasan ya faɗi yayin da ake zagaye kuma rai ya yi halinsa bayan wasu yan mintuna da faruwar haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel