Gobara Ta Kama Wani Kamfanin Takalma Na ’Yan China a Jihar Ogun
- Yanzu muke samun labarin cewa, wata gobara ta kama wani kamfanin 'yan China a jihar Ogun, Kudu maso Yammacin Najeriya
- Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, an ce wutar na ci gaba da ci duk da kuwa jami'an kashe gobara sun hallara
- Mazauna sun shiga tashin hankali yayin da suke tsoron tsillar wutar zuwa wasu gidaje da gine-ginen da ke gefe
Jihar Ogun - Harkokin kasuwanci sun birkice a ranar Litinin a ASCON kusa da Ibafo, a kan titin Legas zuwa Ibadan yayin da gobara ta kama wani kamfanin 'yan China da ke yankin.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, gobarar ta jawo damuwa tsakanin mazauna yankin.
Daga baya an gano cewa, kamfanin na 'yan China yana kera jakukkuna, takalma da leda ne.
Da misalin karfe 5 na yamma, wakilin jaridar ya ziyarci yankin, ya kuma ga har zuwa lokacin kamfanin na ci da wuta duk da kuwa jami'an kwana-kwana sun kawo dauki.
Yadda Wata Budurwa Yar Shekara 18 Ta Kashe Jaririnta Da Wuka Bisa Shawarar Mahaifiyarta Yar Shekara 60
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mazauna yankin sun bayyana damuwa bayan ganin yawan wutar da ta kama, inda suka bayyana tsoron cewa, akwai yiwuwar ta tsilla zuwa wasu gine-gine da ke zagayen yankin idan ba a shawo kanta ba.
Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Ogun, Fatai Adelafa ya bayyana cewa, jami'ansa na ci gaba da kokarin ganin an kashe wutar, Punch ta ruwaito.
Ya ce:
"Muna sane da lamarin kuma muna yin duk mai yiwuwa wajen kashe wutar."
Gobara ta kama a jihar Kano, makarantar Tsangaya ta kone kurmus
A wani labarin kuma, kunji cewa, wata mummunar gobara ta kama a wata makarantar tsangaya a jihar Kano, Arewa maso Yammacin Najeriya.
An ce dukkan kayan daliban da ke marakantar ya kone, amma gwamnatin jihar ta gaggauta kawo daukin kayan abinci da na sakawa garesu.
Legit.ng Hausa ta tattauna da wani mazaunin yankin da ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana irin daukin da aka kawo makarantar.
Ya ce, an kawowa dukkan dalibai kayan sakawa, tabarmai, bargo da dai sauran amfanin yau da kullum.
Baya ga tallafin gwamnatin jihar, an ce shugaban karamar hukumar ya kawo tallafin kayan sakawa ga daliban.
Ana yawan samun gobara a yankuna daban daban a Najeriya.
Asali: Legit.ng