Kaduna: Jiragen NAF Sun Halaka ‘Yan Bindiga, Wasu da Aka Sace Sun Shaki Iskar ‘Yanci

Kaduna: Jiragen NAF Sun Halaka ‘Yan Bindiga, Wasu da Aka Sace Sun Shaki Iskar ‘Yanci

  • Sojin saman Najeriya sun kaddamar da sintiri tare da kakkabe maboyar ‘yan ta’adda a fadin jihar Kaduna kuma an samu nasara mai tarin yawa
  • A samamen da suka kai, sun yi ruwan wuta kan wasu ‘yan bindigan a Karawa dake Igabi kuma sun yi nasarar ceto wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa dasu
  • Sintirin nasu ya ratsa har zuwa Chikun da Birnin Gwari inda aka ga wasu titunan da dajikan lafiya kalau wanda hakan ke tabbatar da tsaron yankin

Kaduna - Jiragen sojojin saman Najeriya sun yi sintirin sama inda suka gano maboyar ‘yan bindiga a yankin Karawa dake karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna inda suka halaka ‘yan bindiga masu yawa tare da ceto wadanda aka yi garkuwa dasu.

Jiragen sojin sama
Kaduna: Jiragen NAF Sun Halaka ‘Yan Bindiga, Wasu da Aka Sace Sun Shaki Iskar ‘Yanci. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Kwamishinan cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da wannan cigaban a wata takarda da aka fitar a yammacin Litinin.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Najeriya Sun Tarwatsa Sansanonin ‘Yan Bindiga, Sun Halaka 2 a Kaduna

Kamar yadda Aruwan ya bayyana a shafinsa na Twitter, a yankin Kawara dake karamar hukumar Igabi, an tabbatar da mutuwar ‘yan bindiga uku sannan wasu da aka yi garkuwa dasu sun tsere daga yankin kamar yadda majiya mai karfi ta tabbatar.

Majiyar tace a Walawa, karamar hukumar Giwa, an tabbatar da wata maboyar ‘yan bindiga tare da samar mata ruwan bama-bamai cike da nasara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A karamar hukumar Chikun, Aruwan yace an duba Fake, Kangon Kadi, Damba, Unguwar Turai, Galbi, Gwagwada da kewaye. An hango ‘yan ta’addan a kusan nisan kilomita 4 arewa maso yammacin Godani kuma an halaka su.

A cewar Aruwan:

“A Kuduru, wani wurin da ya zama sansanin ‘yan ta’addan an hango su tare da harba musu roka.
“A karamar hukumar Igabi, an kaddamar da ayyuka a Riyawa, Alhaji Isiaka, Rima, Riyawa, Rumana, Ungwan Liman, Mai Gishiri da yankin filin jirgin sama na Kaduna, babu alamun ‘yan ta’addan. Wannan makamancin lamarin ne ya faru a Sabon Birni, Anaba, Malumi, Wusono da Kerawa.

Kara karanta wannan

Ya Hada Baki Wajen Garkuwa Da Matar Ubangidan Yayansa, Ya Kashe Kudin Fansa Kan Yan Mata

“Hakazalika, sintirin ya hada da babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja da layin dogo tare da Jere, Katari, Gonar Olam, Gwagwada, Sarkin Pawa, Abulo, Mangoro, Chikwale da kewaye. An ga ababen hawa na kaiwa da kawowa babu wata barazanar tsaro.”

An samu tsaro a wasu yankunan

Ya kara da cewa:

“Hakazalika an duba babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari tare da yankunan da suka hada da Buruku, Labi, Udawa, Manni da Polewire zuwa Kajuru, Jaka da Rabi da Maguzawa.
“An ga kaiwa da kawowar jama’a kamar yadda aka saba a Kajuru, Kankomi, Kutura, Kuzo, Ungwan Magami da yankunan Ruga.”

Gwamna ElRufai ya yaba

“Gwamnan jihar Kaduna ya samu bayanai cike da godiya tare da yabo ga sojojin.
“Za a cigaba da sintiri ta kasa da ta sama a wadannan wuraren.”

- Kwamishinan Aruwan ya tabbatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng