Sojoji Sun Kakkabe Sansanonin ‘Yan Ta’adda, Sun Dakile Hari Tare da Halaka 2

Sojoji Sun Kakkabe Sansanonin ‘Yan Ta’adda, Sun Dakile Hari Tare da Halaka 2

  • Sojojin Najeriya sun dakile harin ba-zata da ’yan bindiga suka kai musu a sansaninsu dake aka Kankomi na karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna
  • Dakarun sun ragargaji ‘yan bindigan inda suka bibiyesu har zuwa sansanoninsu tare da halaka 2 daga ciki sannan suka samo makamai da babura
  • Sai dai cike da abun takaici, ‘yan bindigan sun halaka wasu mutum 3 a kan hanyarsu ta tserewa daga rugugin luguden wutan sojojin

Kaduna - Dakarun sojin Najeriya a sa’o’in farko na ranar Lahadi, 13 ga watan Nuwamban 2022 a Kankomi dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna sun dakile farmakin ‘yan bindiga tare da halaka daya daga cikinsu yayin da sauran suka tsere da miyagun raunika.

‘Yan bindigan Kaduna
Sojoji Sun Kakkabe Sansanonin ‘Yan Ta’adda, Sun Dakile Hari Tare da Halaka 2. Hoto daga @ZagazOlamakam
Asali: Twitter

Zagazola Makama sun rahoto cewa, maharan sun yi yunkurin fadawa gidajen dakarun sojin. Cike da kwarewa da sanin makamar aiki dakarun suka saki ruwan wuta wanda aka yi sama da awa daya ana yi tsakanin sojojin da ‘yan ta’addan.

Kara karanta wannan

Hotunan Matashin da Ya Kera Masallacin Karamin Masallacin Ka’aba a Borno Ya Birge Jama’a

Wannan yayi sanadiyyar mutuwar daya daga cikin ‘yan ta’addan wanda ke sanye da kayan sojoji kamar yadda hotunan suka nuna.

Sauran sun tsere da raunikan harsasai sakamakon jinin da aka gani a hanyar da suka bi suka tsere.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dakarun sun samo bindiga kirar AK 47, harsasai bakwai da gurneti biyar daga ‘yan bindigan.

Abun takaicin shi ne, yayin da sojojin suka bi ‘yan bindigan da suka tsere, an tsinta gawawwaki uku wanda ya nuna cewa mazauna yankin ne aka kashe.

Soji sun kakkabe sansanonin ‘yan bindiga

A wani cigaba, dakarun rundunar Operation Forest Sanity sun aiwatar da sintiri wurin yankunan Gwagwada zuwa Chikun zuwa Sarkin Pawa har zuwa karamar hukumar Chikun.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, an ci karo da ‘yan ta’addan gaba da Kafaiyo. Daya daga cikin ‘yan ta’addan ya sheka lahira kuma an samo bindiga kirar AK47.

Kara karanta wannan

Rayuka 7 Sun Salwanta a Arangamar Sojoji da ‘Yan Bindiga a Kauyen Gwamnan Anambra

Har ila yau, ‘yan ta’adda biyu sun tsere baya sun ga sojojin inda suka bar baburan da sojojin suka kwashe. Sojojin sun tarwatsa sansanonin ‘yan ta’addan dake Kafaiyo, Dafako, Kopi da Gadani.

Gwamna yayi ta’aziyya

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir ElRufai ya samu labarin cike da takaici inda ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu yayin da yake fatan rahama ga mamatan.

Gwamnan ya mika godiyarsa ga zakakuran sojojin kan kokarinsu da sadaukarwarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel