Yan Bindiga Sun Harbe Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Har Lahira a Nasarawa

Yan Bindiga Sun Harbe Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Har Lahira a Nasarawa

  • Wasu miyagu sun kashe matar wani tsohon shugaban ƙaramar hukuma a jihar Nasarawa ranar Litinin
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun buɗe wa motar da matar ke ciki yayin da take kan hanyar zuwa kasuwar Assakio
  • Marigayyar ta kasance sananniyar yar kasuwa kuma tana da 'ya'ya biyu, an kai gawarta ɗakin ajiyar gawarwaki

Nasarawa - 'Yan bindiga sun harbe matar tsohon shugaban ƙaramar hukuma har lahira a jihar Nasarawa, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Rahotanni sun ce matar mai suna, Astira Akolo Ahmed Success, na kan hanyar zuwa kasuwar Assakio lokacin da maharan suka farmaketa da ƙarfe 9:00 na safiyar Litinin a Titin Lafia- Shendam.

Matsalar yan bindiga.
Yan Bindiga Sun Harbe Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Har Lahira a Nasarawa Hoto: vanguardngr
Asali: Twitter

Wasu bayanai da wakilin jaridar ya tattara a Lafiya, babban birnin jihar sun nuna cewa Misis Success na zaune a ɓangaren Fasinjoji lokacin da 'yan bindigan suka buɗe wa motarsu wuta.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Samu Gagarumin Goyon Baya, Dubbannin Kusoshin APC da LP Sun Koma PDP a Jihar Arewa

An ce maharan sun nufi Direban motan ne yayin da wani Harsashi ya sameta kai tsaye kuma ya yi ajalinta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har zuwa numfashinta na ƙarshe, Misis Success ta kasance sananniyar yar kasuwa kuma tana da 'ya'ya biyu da Allah ya azurtata da su.

A halin yanzun, an ɗauki gawarta zuwa ɗakin ajiye gawarwaki kafin iyalanta su gama shirye-shiryen yi mata jana'iza.

Matsalar 'yan bindiga na ɗaya ɗaga cikin kalubalen da Najeriya ke fama da su a fannin tsaro musamman a arewacin Najeriya.

Ana neman yan bindiga 19 ruwa a jallo

A yau Litinin, Hedkwatar tsaro ta ƙasar nan ta fitar da jerin sunayen hatsabiban 'yan bindiga da ake nema ruwa a jallo, waɗanda suka addabi arewa maso gabas, arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.

Bugu da ƙari tace zata baiwa duk wanda ya taimaka da bayanai har aka kama 'yan ta'addan tukuicin naira Miliyan N5m. Ta nemi duk me bayani ya tuntuɓe ta a wannan lambar 09135904467.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wasu Fitattun Malamai Biyu a Jihar Arewa

A wani labarin kuma Yan bindiga sun yi barazanar matsa wa gwamnan jihar Anambra har sai ya yi murabus daga kujerarsa

A wani sakon murya da jaridar The Nation ta ruwaito, wani kwamandan mayaƙan ESN yace tun da gwamnan ya zaɓi matsa musu da jami'an tsaro to zasu canza salo.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Ikenga Tochukwu, yace har yanzun sakon bai iso teburinsa ba, ya nemi duk mai muryar ya kai rahoto Caji Ofis mafi kusa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262