Mun Daina Karban Naira Yanzu: Yan Ta'addan ISWAP Ta Bayyanawa Mutane

Mun Daina Karban Naira Yanzu: Yan Ta'addan ISWAP Ta Bayyanawa Mutane

  • Yan ta'addan da suka addabi Arewa maso gabashin Najeriya sun ce zasu daina karban haraji a Naira
  • Yan ta'addan suna karban haraji hannun manoma, masunta, da masu kiwo a tafkin Chadi
  • ISWAP na niyyar kafa daular Musulunci a yankin yammacin nahiyar Afrika

Majalisar Shura ta kungiyar yan ta'addan ISWAP ta sanar da cewa ta daina karban kudin Naira daga wajen Manoma da Masuntan dake biyanta haraji saboda shirin sauya fasalin Naira da gwamnatin Najeriya tayi.

Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, ta yanke shawara sauya fasalin kudin Naira na N200, N500, N1000 kuma za'a daina amfani da tsohon takardar ranar 31 ga Junairu, 2023.

Zagazola Makama ya ruwaito cewa wannan abu ya tada hankulan yan ta'addan ISWAP dake yankin Tumbus na tafkin Chadi.

Makama ya ce majiya mai karfi ta laburta masa cewa yanzu yan ta'addan kudin CFA Franc suke karba domin rage asara.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma, Yadda Wata Budurwa Ta Fada Tekun Lagas Akan Saurayi

ISAWP
Mun Daina Karban Naira Yanzu: Yan Ta'addan ISWAP Ta Bayyanawa Mutane
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyin sun kara da cewa yan ta'addan sun hana manoma, masunta da masu kiwo shiga tafkin Chadi ta Marte, Abadam, da Gamboru Ngala domin taikata shigo da Naira sansanin yan ta'addan.

Kwamandojin ISWAP masu hakkin karban haraji, Ibn Umar da Malam Ba'ana ne suka kafa wannan sabuwar Doka.

Yanzu sun kafa sabbin hanyoyi ta Kamaru (Bulgaram, Cikka, Guma, Maltam, Doron Liman da Ramin Dorina)

Yanzu ISAWP ta koma karban CFA Francs 1,500 matsayin kudin harajin wata da take karba hannun mutane.

Akan Sauya Fasalin Naira, Ba Zamu Fasa Ba: Shugaba Buhari Ya Bayyana A Landan

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya bayyana a Landan cewa tattalin arzikin Najeriya zai amfana matuka da sauya fasalin Naira da za'ayi a watan Disamba.

Buhari ya ce babu ja da baya game da lamarin sauya fasalin takardun kudin Najeriya 'Naira'.

Kara karanta wannan

Almundahanar N19m: EFCC Ta Damke Odito-Janar A Jihar Yobe, An Kwace Kadarorinsa 5

Shugaba Buhari yace:

"Sauyin nan da za'a yi, na san kudade da yawa zasu fuskanci matsala amma lokacin da aka bada daga Oktoba ne zuwa Disamba."

"Watanni uku sun isa amfani da duka kudin da kake da su, ka kaisu banki. Saboda haka ban san dalilin da ya sa mutane ke korafi ba. Babu Gudu, babu ja da baya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel