Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ya Birne Ɗansa, Manyan Ƴan Siyasa Sun Halarci Jana'izar Don Yin Bankwana
- An yi jana'izar Tunde Mark, dan tsohon shugaban majalisar dattawar Najeriya David Mark a Otukpo, jihar Benue
- Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue da wasu manyan yan siyasa suna cikin wadanda suka halarci jana'izar
- Tunde Mark wanda ya rasu yana da shekaru 51 a duniya, manarci ne mai daraja wanda ya halarci makarantun kasashen waje da dama, ciki har da Harvard da Kwalejin Imperial
Benue, Otukpo - Bakin ciki da radadi da ke tattare da mutuwar 'ya'yan mutum ya fi tsananta a lokacin da ake birne 'ya'yan.
Hakan ta faru a Otukpo, fitaccen gari a jihar Benue inda fitattun mutane a kasar suka taru don nuna girmamawa ta karshe ga babban dan tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, a ranar Juma'a, 11 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Ortom ya yi bankwana ta karshe
Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue na cikin manyan mutanen da suka jagoranci manyan yan siyasa da suka halarci jana'izar mamacin.
Da ya ke jawabi a wurin taron jana'izar, Gwamna Ortom a gidan tsohon shugaban majalisar dattawar, ya ce marigayi Tunde Mark mutum ne mai halin girma wanda ya taka muhimmin rawa wurin ayyukan da mahaifinsa ya yi a matsayin shugaban majalisa.
Kamar yadda The Nation ta rahoto, Gwamna Ortom ya yi addu'a Allah ya bawa iyalan hakuri da juriya rashin ya kuma basu kwanciyar hankali a zukatansu da rayuwarsu.
Mataimakin Ortom, Abounu shima ya yi bankwana da marigayin
A bangarensa, mataimakin gwamna, Benson Abounu, ya ce kowa na kaunar marigayi Tunde saboda yadda ya ke mu'amula da dukkan mutane ba tare da nuna banbanci ko wariya ba.
Ya bukaci iyalan kada su kasance cikin kunci yana mai cewa:
"Allah da ya kawo shi duniya ya san dalilin da yasa ya dauke shi a wannan lokacin."
Sanata Patrick Aba Moro shima ya yi jawabin bankwana ga marigayi Tunde wanda ya ce ya yi rayuwa mai amfani kuma mutane da dama za su yi kewarsa cewa shugaba mai tasowa kamarsa ya rasu.
A cewar The Nation, ya mika ta'aziyarsa ga iyalan ya kuma ce zai saka su a addu'a.
Ya yi kira ga iyalan su yi murna domin mariyagin ya kawo sauyi mai amfani a rayuwar mutane.
Hotuna: An yi jana’izar shahararren jarumin Kannywood, Umar Malumfashi, Ya Yi Jama’a Sosai
A wani rahoton, kun ji cewa a ranar Laraba, 28 ga watan Satumba ne aka yi jana’izar shahararren jarumin Kannywood, Umar Malumfashi, a jihar Kano.
Dandazon jama’a da manya-manyan jaruman masana’artan sun samu halartan jana’izar marigayin inda aka sada shi da gidansa na gaskiya.
Asali: Legit.ng